Sarrafa amfanin gona a gida ne ginshiƙin wadatar abinci a Nijeriya – Tajudeen

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kakakin Majalisar Wakilan Tarayyar Nijeriya, Hon. Abbas Tajudeen, ya sake jaddada aniyar Majalisar Dokokin Tarayya na samar da cikakken goyon baya da kariya ga ’yan kasuwa da masu zuba jari na cikin gida da ke taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa masana’antu da samar da kayayyaki a Nijeriya.

Kakakin ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin bikin ƙaddamar da sabuwar masana’antar Simkay Foods Limited da za ta riƙa sarrafa masara tare da samar da garin masara da kuma abubuwan da suka shafi masara na masara a yankin Zazzau Industrial Park and Industries (ZIPI) da ke Zariya, Jihar Kaduna.

Abbas ya yi kira ga ’yan kasuwa na cikin gida da na ƙasashen waje da su ƙara zuba jari cikin masana’antun Nijeriya, yana mai cewa akwai muhimmiyar dama ga masu zuba jari a fannin sarrafa kayayyakin noma da sauran masana’antun cikin gida.

Ya jaddada cewa wadatar abinci tana da alaƙa kai tsaye da tsaron ƙasa, saboda haka ya ce wajibi ne Nijeriya ta sauya salon tattalin arzikinta daga fitar da albarkatun gona ɗanye zuwa sarrafa su a cikin gida.

A cewarsa, sarrafa masara a cikin gida na taimakawa wajen riƙe darajar tattalin arzikin amfanin gona a cikin ƙasa, rage asarar amfanin gona bayan girbi, da daidaita farashin kayayyaki a kasuwa. Ya ƙara da cewa, hakan zai samar wa manoma kasuwa tabbatacciya, tare da ƙarfafa sarkar samar da kayayyakin noma daga gona zuwa masana’anta.

Kakakin Majalisar ya ce sabuwar masana’antar ta Simkay za ta ƙara ƙarfafa wannan sarkar tattalin arziki, ta hanyar ƙara wa manoman karkara samun kuɗaɗen shiga, samar da ayyukan yi kai tsaye da kuma waɗanda ba kai tsaye ba ga matasa, tare da taimakawa wajen sauya fasalin tattalin arzikin yankin Arewa maso Yamma.

Da yake magana kan rawar da Majalisar Wakilai za ta taka, Abbas ya ce majalisar za ta ci gaba da samar da yanayin da ya dace da kasuwanci ta hanyar kafa dokoki masu tallafa wa masana’antun cikin gida da kuma inganta sa ido kan yadda ake aiwatar da su.

Ya yi nuni da sauye-sauyen haraji da aka aiwatar a baya-bayan nan, yana cewa an tsara wasu daga cikin sauye-sauyen ne domin sauƙaƙa wa masu masana’antun cikin gida gudanar da harkokinsu da kuma ƙarfafa samar da kayayyaki a Nijeriya.

Haka kuma, ya ce wasu manyan ayyukan raya ababen more rayuwa a yankin, ciki har da Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma da kuma bututun iskar gas na AKK, za su taimaka wajen ƙara wa yankin ƙarfin masana’antu.

Abbas ya kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa manufofin sake fasalin tattalin arzikin ƙasa da gwamnatinsa ke aiwatarwa, yana mai cewa irin waɗannan sauye-sauye na da muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa masana’antun cikin gida da jawo sabbin jarin kuɗi.

Haka zalika, ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kaduna bisa samar da yanayin da ya dace da zuba jari daga kamfanoni masu zaman kansu, yana mai cewa haɗin gwiwar gwamnati da masu zuba jari na da muhimmiyar rawa wajen cimma ci gaban masana’antu da tattalin arziki mai ɗorewa.

By ukarofi

Leave a Reply