
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya buɗe yaƙin neman zaɓensa a hukumance na takarar kujerar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027 a hukumance, inda ya yi alƙawarin mayar da ababen da ke damun ‘yan Nijeriya na yau da kullum a matsayin jigon yawon neman zaɓen nasa.
Obi ya bayyana haka ne a birnin Onitsha da ke Jihar Anambara, inda ya ƙalubalanci sauran ‘yan takara da su fito su kare tarihin ayyukansu na baya da yin bayanin abin da ya sa suka cancanci jagorancin Nijeriya. Ya ce, kada a riƙa tilasta wa ‘yan Nijeriya dogara da kalaman ‘yan takara wajen yanke hukunci kan wanda za su zaɓa yayin zaɓe.
Tsohon gwamnan na Anambara ya kuma ce shugabanci nagari na buƙatar jagorori su fahimci ainihin abin da ‘yan ƙasa talakawa suke fuskanta, musamman ƙauyukan da ke fuskantar ƙalubalen matsalolin rashin tsaro, talauci da annobar ambaliya da makamantansu. “Ba za ka iya shugabantar mutanen da ba ka iya ziyartarsu, saurare ko fahimtar su ba,” inji Obi.
Obi, wanda ke neman kujerar shugaban ƙasa tare da abokin tafiyarsa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce za su dama da ‘yan Nijeriya daga sassan ƙasar daban-daban a maimakon dogara da wakilci a madadinsu wajen yawon neman zaɓe.
Ya bayyana zaɓen na 2027 a matsayin dama ga masu zaɓe na su tabbatar da yin nazari kan tarihi, tsare-tsare da zimmar ‘yan takarar da suke neman jagorantar ƙasar domin samar da shugabanci nagari a ƙasarsu.
A cewarsa, Nijeriya na fuskantar matuƙar matsin ƙalubale a harkar tattali da tsaro, ciki har da talauci, rashin tsaron abinci, rashin aiki, rashin wadatar ababen more rayuwa, rashin isasshen lantarki da tsadar gudanar da harkokin kasuwanci.
Akan haka ne ta ya ci alwashin shawo kan matsalolin da ke haddasa ƙalubalen da ‘yan Nijeriya suke fuskanta a fannoni daban-daban ta yadda zai samar da yanayi da tsari mai kyau wajen ganin Nijeriya ta farfaɗo daga halin matsin rayuwa da ta tsinci kanta aciki muddin aka zaɓe shi a matsayin shugaba a 2027.
