An karrama Dakta Margaret da lambar yabo ta kwamishiniya mafi hazaƙa a Nijeriya

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

An karrama kwamishiniyar muhalli da albarkatun ƙasa na gwamnatin jihar Nasarawa gimbiya Dr. Margaret Elayo da lambar yabo na musamman wato kwamishiniya wace tayi zarra a ƙwarewa da aiki tuƙuru da kuma hidima na musamman ga mutane.

An bai wa kwamishiniyar wannan karramawar ne a wani babban taro da Arewa Media Publications ta shirya a ranar Alhamis na makon da ake ciki inda kuma har aka ba ta lambar yabo na International Merit Award for Excellence in Leadership a turance ta shekarar 2026.

Wato dai hakan na nufin kamar yadda ake ce wa ne “kifi na zinariya ba ya ɓoyuwa.” Haƙika sadaukarwa da jajircewar Dr. Elayo ba su tafi a banza ba.

Wasu majiya a jihar sun ce tabbas waɗannan lambobin yabo na musamman da aka ba ta sun ƙara mata kuzari da ƙwarin gwiwa na yin amfani da gogewarta mai yawa wajen isar da ingantaccen jagoranci domin cigaban jihar ta Nasarawa.

Da yake jawabi Prince Joshua Adeleke wato shugaban Arewa Media Publications ya tabbatar da cewa wannan karramawa ba ta ba shi mamaki ba ganin yadda tarihi da ayyukan agaji da Dr. Elayo ke yi.

Ya ce sakamakon wani tantancewarsu mai zurfi ce wadda ta haɗa da ziyarar jihohin ƙasar nan daban-daban da tattaunawa da jama’a inda duka kuma sun gano cewa jagorancin Dr. Margaret Elayo ya yi fice kuma babu wanda ya kai ta cikin kwamishinonin ƙasar nan.

“Wannan lambar yabo ta cancanta ce wadda ita Dr. Ilayo ta cancanta kuma ba tare da kuɗi ko wani tasiri na waje ba. Kimar mu ta tsawon mako guda a jihar Nasarawa ta sa mu cimma matsaya cewa sunanki ya zama sananne a ko ina a nan,” in ji Adeleke.

Adeleke ya ƙara yaba wa Dr. Elayo bisa nuna misalin jagoranci mai karfi ta hanyar shiga ayyukan tsaftace muhalli da kanta abin da ya bayyana shi a matsayin “mai ban mamaki kuma ya kamata a yi koyi da ita.”

Baya ga karrama Dr. Elayo, Arewa Media Publications ta kuma bai wa ma’aikatar ta muhalli da albarkatun ƙasa wani lambar yabon ta Outstanding Achievement Award shima a turance wato a matsayin ma’aikata mafi hazaƙa a faɗin Najeriya baki ɗaya na shekarar 2026.

A cikin jawabinta na karɓar lambar yabon Dr. Margaret Elayo ta bayyana godiyarta na musamman bisa wannan karramawa. Tace tabbas ta sadaukar da lambar yabon ga jami’ai da ma’aikata masu aiki tuƙuru na ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasa na jihar tare da yaba musu bisa goyon bayan da suka ba ta a tafiyarta a ko yaushe inda ta kuma yi amfani da damar ta yaba wa gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule game da cikakken goyon baya da yake bai wa ma’aikatar don basu damar cimma buri.

Shi kuma a nasa ɓangaren da yake tattaunawa da wakilin mu game da karramawar, Kwamaret Ibrahim Abdul wanda shine mai taimaka wa kwamishiniyar na musamman akan harkokin yaɗa labarai yace ” Tabbas ina bayyana maka cewa wannan karramawa ba wai nasarar Dr. Elayo kaɗai ta nuna ba, ta ma nuna ƙoƙarin haɗin gwiwa na tawagarta ne wajen inganta harkokin kiyaye muhalli da albarkatun ƙasa a jihar ta Nasarawa baki ɗaya.” Inji shi.

By ukarofi

Leave a Reply