Jihar Neja ta yi gargaɗin tsagewar madatsar ruwan Kaduna da barazanar ambaliya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ta yi gargadi kan rahotannin samun matsala da kuma tsagewar ginin Madatsar Ruwan Kangimi da ke ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna, tana mai cewa lalacewar madatsar na iya jefa al’ummomin da ke ƙasa cikin haɗarin ambaliya.

Darakta-Janar na NSEMA, Abdullahi Arah, ya bayyana damuwar hukumar a cikin wata sanarwa, inda ya yi kira da a gaggauta gudanar da cikakken binciken fasaha kan madatsar tare da ɗaukar matakan kariya.

Ya ce lamarin na buƙatar kulawa cikin gaggawa musamman ganin cewa damina na ci gaba da gudana, yayin da haɗarin ambaliya ke ƙaruwa a sassa daban-daban na ƙasar.

Arah ya bayyana cewa idan madatsar ta samu babbar matsalar tsari ko kuma ta rushe, hakan na iya haifar da sakin ruwa mai yawa cikin gaggawa, wanda zai iya janyo ambaliya tare da lalata gidaje, ababen more rayuwa da sauran dukiyoyin al’ummomin da ke ƙasa da madatsar.

Saboda haka, NSEMA ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin Jihar Kaduna, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta ƙasa (NEMA), hukumomin da ke kula da madatsun ruwa, Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa ta Nijeriya, Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet) da hukumomin tsaro da su gaggauta tantance yanayin madatsar tare da tabbatar da matakan da suka dace.

Hukumar ta kuma buƙaci a gudanar da cikakken bincike kan haɗarin ambaliya a yankunan da ke ƙasa da madatsar, tare da gano al’ummomin da ke cikin haɗari da muhimman ababen more rayuwa da ka iya fuskantar barazana.

NSEMA ta ce ya kamata hukumomin da abin ya shafa su samar da ingantaccen tsarin gargadin jama’a tun da wuri, da kuma shirye-shiryen kwashe mutane idan lamarin ya tsananta.

Ta kuma buƙaci a ware wuraren da jama’a za su koma idan aka samu ambaliya, tare da bayyana hanyoyin da za a bi wajen kwashe su cikin gaggawa.

Hukumar ta jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin jihohin Kaduna da Neja da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja, da sauran yankunan da ka iya fuskantar illar ambaliyar, domin tabbatar da samun haɗin kai wajen mayar da martani idan matsalar ta tsananta.

NSEMA ta shawarci mazauna yankunan da ka iya fuskantar haɗarin da su kwantar da hankalinsu, amma su kasance cikin shiri, tare da guje wa ayyukan da ba dole ba a kusa da magudanan ruwa musamman lokacin da ake ruwan sama mai ƙarfi.

Hukumar ta kuma buƙaci jama’a da su riƙa bin bayanan hukuma daga hukumomin da abin ya shafa, tare da sanin wuraren da za su iya tserewa zuwa da hanyoyin fita daga yankunansu idan aka samu ambaliya.

NSEMA ta ce rigakafi da shiri tun da wuri su ne mafi muhimmanci wajen kare rayuka da dukiyoyi, tana kira ga hukumomin da abin ya shafa da su ɗauki matakan da suka dace kafin yiwuwar afkuwar wani bala’i da madatsar ruwan zai iya haddasawa.

By ukarofi

Leave a Reply