Yadda aka yi gagarumin bikin Blueprint na shekara

Spread the love

*Kutsen yanar gizo ne babbar barazana ga sahihancin zaɓe – Janar Musa

*Bai kamata rashin tsaro ya kawo cikas ga sahihancin zaɓe ba – Yari

*Girmamawar Blueprint za ta zaburar da waɗanda aka karrama – Salisu Umar

*Gwamna Dauda na Zamfara ya yi zarra a cikin gwamnoni

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A ranar Talata, 18 ga Agusta, 2027, kamfanin buga jaridun Blueprint da Manhaja ya gudanar da gagarumin bikin shekara na karrama waɗanda suka yi fice a fannoni daban-daban a Nijeriya cikin shekarar da ta gabata ta 2025, inda aka yi bikin a Babban Birnin Tarayya Abuja a Babban ɗakin Taro na ƙasa da ƙasa na Bola Ahmed Tinubu.

Wasu daga cikin waɗanda aka karrama ɗin sun haɗa da Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, Gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal da sauransu. Sai dai kuma, baya ga bayar da lambobin yabo ga waɗanda aka karrama a taron, an kuma gabatar da ƙasidu da maƙaloli a wajen taron.

Kutsen yanar gizo ne babbar barazana ga sahihancin – Janar Musa

Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), ya bayyana hare-haren yanar gizo a matsayin babbar barazana ga tsaron zaɓe, yana mai cewa yanayin barazanar tsaro ya sauya daga hare-haren zahiri zuwa na yanar gizo.

Musa ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake gabatar da babban jawabi a taron lacca na 8 na Blueprint Newspapers Public Lecture, Impact Series and Awards, wanda taken taronsa shi ne “ƙalubalen Tsaro da Sahihancin Zaɓen Nijeriya na 2027.” Wakilinsa, mai ba shi shawara kan manufofi da bincike, Manjo Janar Olufemi Akinjobi (mai ritaya), ne ya gabatar da jawabin.

Ministan ya ce a yau babbar barazana ga zaɓe ba lallai ta kasance mutum ɗauke da makami a kusa da rumfar zaɓe ba, domin mai kai hari na iya kasancewa a bayan kwamfuta yana yaɗa bayanan ƙarya, amfani da rarrabuwar kawuna da kuma ƙoƙarin rage amincewar jama’a da hukumomin dimokuraɗiyya.

Ya ce saboda haka, tsaron zaɓe bai kamata ya tsaya kawai kan kare rumfunan zaɓe ba, sai ya haɗa da kare tsarin dimokuraɗiyya, ƙarfafa tsaron yanar gizo, sadarwa mai inganci da kuma kare sahihancin bayanai.

Musa ya ce ci gaban fasahar zamani, musamman ƙwarewar na’urorin basirar wucin gadi (AI), ya samar da damammaki masu yawa ga ci gaba da inganta shugabanci, amma a lokaci guda ya ƙirƙiri sabbin barazanar da za su iya yin illa ga zaɓe. Ya ce, a yanzu ana iya ƙirƙirar bidiyoyi na ƙarya masu kama da na gaskiya, kwaikwayon muryoyin mutane da kuma sauya hotuna ta yadda za a iya yaudarar miliyoyin mutane cikin ƙanƙanin lokaci.

Ya bayyana cewa a wasu ƙasashe an riga an ga yadda yaɗa bayanan ƙarya, katsalandan ta yanar gizo da kuma yaɗa munanan abubuwan dijital suka yi tasiri ga zaɓe tare da rage amincewar jama’a da tsarin dimokuraɗiyya, yana mai cewa Nijeriya ma ba ta tsira daga irin wannan barazana ba.

Duk da haka, ministan ya yaba wa Nijeriya kan juriyar da ta nuna wajen kare tsarin dimokuraɗiyya tun bayan komawar mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999. Ya ce kowane zagayen zaɓe ya zo da sabbin ƙalubale, amma hakan ya taimaka wajen ƙara wa hukumomin ƙasar ƙwarewar tinkarar barazanar tsaro.

Ya ce zaɓen 2023 ya nuna irin ci gaban da aka samu, duk da cewa akwai wuraren da aka samu wasu matsaloli. A cewarsa, hukumomin tsaro sun gudanar da ɗaya daga cikin manyan tsare-tsaren tsaron zaɓe da aka taɓa aiwatarwa a tarihin dimokuraɗiyyar Nijeriya, tare da haɗin gwiwar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) da sauran masu ruwa da tsaki.

Musa ya jaddada cewa tsaron zaɓe ba abu ne da ake shirya shi a ranar zaɓe kawai ba, domin yana buƙatar shiri na tsawon watanni, tattara bayanan sirri, ayyukan tsaro bisa bayanan sirri, haɗin gwiwa tsakanin hukumomi, ingantacciyar sadarwa da kuma ci gaba da tantance sabbin barazanar da ke kunno kai. Ya ce, yayin da barazanar zaɓe ke sauyawa, dole ne hanyoyin da ake amfani da su wajen tunkarar su su ma su sauya.

Dangane da zaɓen 2027, ministan ya ce bai kamata a ɗauke shi a matsayin wani aikin tsaro na ranar zaɓe kawai ba, sai dai a matsayin wani muhimmin aiki na ƙasa da zai ƙarfafa juriyar tsarin dimokuraɗiyya, hukumomi su iya tinkarar matsin lamba ba tare da keta kundin tsarin mulki ba, sannan jama’a su iya ƙin yarda da bayanan ƙarya tare da ci gaba da amincewa da tsarin dimokuraɗiyya. Musa ya kuma bayyana cewa babu wata hanyar tsaro, komai ingancinta, da za ta iya tabbatar da zaɓe cikin lumana idan ’yan siyasa suka zaɓi tashin hankali maimakon tattaunawa.

Ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da su fifita muradun ƙasa kan ribar jam’iyya, yayin da ’yan takara kuma ya kamata su fahimci cewa fafatawar siyasa ba yaƙi ba ce.

Ministan ya gabatar da wasu muhimman matakai shida da ya ce za su taimaka wajen ƙarfafa tsaron zaɓe gabanin 2027. Matakan sun haɗa da haɗa bayanan sirri na tsaro, tantance barazana, kare ababen more rayuwa na dijital, ƙarfafa tsaron yanar gizon zaɓe, haɗin gwiwar farar hula da sojoji, da kuma samar da ingantacciyar hanyar sadarwa ta bai ɗaya.

Ya tabbatar da cewa Ma’aikatar Tsaro za ta yi aiki kafada da kafada da Ofishin Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (ONSA), Rundunar Sojin Nijeriya, ’Yan Sandan Nijeriya, Hukumar DSS, Hukumar Leken Asiri ta Tsaro (DIA), INEC da sauran hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da cewa an gudanar da ayyukan da aka ɗora wa kowace hukuma bisa ƙa’ida, cikin ƙwarewa da rashin son rai.

Musa ya jaddada cewa Rundunar Sojin Nijeriya ba ta da wata jam’iyya ko ɗan takarar da take goyon baya, yana mai cewa biyayyarta tana ga Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya ne, da kuma al’ummar ƙasar. Ya kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su tabbatar da sahihanci, gaskiya da taka-tsantsan wajen rahotannin zaɓe, yayin da ya buƙaci ƙungiyoyin fararen hula su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a da kuma ƙarfafa shiga harkokin dimokuraɗiyya cikin lumana.

Haka kuma, ya yi kira ga sarakunan gargajiya da shugabannin addinai da su ci gaba da taka rawa wajen sasanta al’umma da rage rikice-rikice, yayin da ya buƙaci matasan Nijeriya da su ƙi amincewa da duk wani yunƙuri na amfani da su wajen tashin hankali ko yaudarar siyasa.

Bai kamata rashin tsaro ya kawo cikas ga sahihancin zaɓe ba – Yari

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Marafan Sokoto, Abdul’Aziz Yari Abubakar, ya yi kira da a gudanar da sahihin zaɓe na gaskiya da adalci a babban zaɓen 2027, yana mai cewa bai kamata rashin tsaro ya lalata sahihancin tsarin zaɓe ba.

Yari ya bayyana haka ne a matsayin shugaban taron lacca na shekara-shekara na Blueprint Newspapers karo na takwas, da aka gudanar a Abuja, mai taken “Kalubalen Tsaro da Sahihancin Zaɓen 2027.”

Ya ce jam’iyyar da ke mulki na da alhakin nuna jajircewarta wajen tabbatar da dimokuraɗiyya ta hanyar tabbatar da cewa zaɓen 2027 ya kasance cikin ’yanci da adalci.

“Daga jam’iyyar da ke mulki, abin da zan tabbatar wa sauran mutane shi ne, duk da ƙalubalen rashin tsaro, sahihancin wannan zaɓe zai kasance cikin abubuwan farko kuma na musamman, da yardar Allah,” inji shi.

Yari ya ce bai ji daɗin abin da ya faru a zaɓen gwamnan Jihar Osun ba, amma ya ce lamarin na iya zama alamar cewa gwamnati na da niyyar tabbatar da sahihin tsarin zaɓe a 2027. Ya ce, babu wani shugaban ƙasa, ko daga Arewa maso Gabas ko Kudu maso Kudu, da zai yarda abin da ya faru a Osun ya sake faruwa, yana mai cewa ya kamata a gudanar da zaɓe cikin ’yanci da adalci. “Duk wanda ya yi nasara, haka ta kasance,” inji Yari.

Da yake magana kan lokacin da yake gwamnan Zamfara tsakanin 2011 zuwa 2019, Yari ya ce ya fuskanci matsalar tsaro kai tsaye, tare da irin ƙalubalen da gwamnatoci daban-daban suka fuskanta wajen magance ta. Ya ce, matsalar tsaro ta kasance babban ƙalubale a lokacin zaɓen 2015, zaɓen sake zaben tsohon Shugaba Muhammadu Buhari a 2019 da kuma babban zaɓen 2023.

A cewarsa, magance rashin tsaro ba aikin hukumomin tsaro na gwamnati kaɗai ba ne, domin ’yan siyasa, manyan mutane da sauran al’umma duk suna da rawar da za su taka wajen kawo ƙarshen matsalar. “Mu ne tsaro, haka kuma mu ne rashin tsaro. Shugabanni da talakawa, ba aikin hukumomin tsaro na gwamnati kaɗai ba ne. ’Yan siyasa, manyan mutane da talakawa duk suna da hannu a ciki,” inji shi.

Yari ya ce matsalar tsaro ta wuce batun zaɓe, domin tana shafar rayuwar ’yan ƙasa, tattalin arziki da jin daɗinsu. Ya bayyana tsaro da tattalin arziki a matsayin manyan abubuwa guda biyu da ya kamata Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da bai wa muhimmanci.

Ya yaba da ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen ƙarfafa tsaro, musamman ƙara yawan jami’an tsaro da samar da kayan aiki, amma ya ce akwai buƙatar ƙarin haɗin kai domin samun zaman lafiya mai ɗorewa.

Tsohon gwamnan ya yi kira ga ’yan Nijeriya da kada su mayar da matsalar rashin tsaro ta siyasa, yana mai cewa ya kamata a ɗauke ta a matsayin matsalar ƙasa baki ɗaya. “Bai kamata mu mayar da shi siyasa ba. Lokacin da na zama gwamna, lokacin da wannan abu ya fara, sun yi ƙoƙarin mayar da shi siyasa. Na ce a’a, wannan ba siyasa ba ce. Wannan abu ya shafi rayuwarmu,” inji shi.

Yari ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su haɗa kai wajen gina ƙasa mai tsaro domin al’ummomin yanzu da na gaba. Ya kuma bayyana fatansa na ganin Nijeriya ta shawo kan ƙalubalen da take fuskanta tare da ci gaba da kasancewa ƙasa ɗaya, yana mai cewa “ba mu da wata ƙasa face Nijeriya.”

Girmamawar Blueprint za ta zaburar da waɗanda aka karrama – Salisu Umar

Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Blueprint Newspapers Ltd, Malam Salisu Umar, ya buƙaci waɗanda aka karrama da lambar yabo ta Blueprint Newspapers ta 2025 da su ɗauki karramawar a matsayin ƙarin ƙwarin gwiwa wajen faɗaɗa ayyukan da suke yi domin ci gaban Nijeriya.

Alhaji Salisu Umar ya bayyana hakan ne ranar Talata a Abuja, yayin bikin Blueprint Newspapers Annual Public Lecture, Impact Series and Awards na shekarar 2025, wanda aka gudanar a Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre.

Daga cikin waɗanda aka karrama da lambar yabon akwai Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda; Gwamnan Jihar Enugu, Peter Ndubuisi Mbah; Gwamnan Sokoto, Ahmad Aliyu; Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal; Gwamnan Taraba, Agbu Kefas; Gwamnan Jigawa, Umar Namadi; da Gwamnan Cross Riɓer, Prince Bassey Edet Otu.

Sauran waɗanda aka karrama sun haɗa da tsohon Gwamnan Bauchi, Mohammed Abdullahi Abubakar; tsohon Gwamnan Zamfara, Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar; Shugaban Kwamitin Kuɗi na Majalisar Wakilai, Hon. James Faleke; da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Olayemi Cardoso, da sauransu.

Yilwatda ya zama gwarzon shekara

Malam Salisu ya ce an zaɓi waɗanda aka karrama ne daga fannoni daban-daban bisa irin gudummawar da suke bayarwa wajen gina ƙasa da bunƙasa tattalin arziki da zamantakewar al’umma.

Ya bayyana cewa an fara gudanar da taron shekara-shekara na Blueprint a shekarar 2018, da nufin samar da wata kafa da za a tattauna muhimman batutuwan ƙasa ta hanyar ilimi da zurfin tunani, ba tare da takaita tattaunawar ga harkar jarida kawai ba. Ya ce taron na kuma da manufar karrama ’yan Nijeriya da suka nuna nagartaccen shugabanci, tsayayyen tsari wajen tsara manufofi da kuma tasiri wajen kawo sauye-sauye a ɓangarorin gwamnati da masu zaman kansu.

Ya ce an zaɓi taken taron na bana, “Kalubalen Tsaro da Sahihancin Zaɓen Nijeriya na 2027”, ne domin mayar da hankali kan tsaron ƙasa da kuma ba da gudummawa ga tattaunawar da ake yi kan matsalar tsaro da ta daɗe tana addabar ƙasar.

Dalilin zaɓen Christopher Musa

Salisu Umar ya ce zaɓen Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), a matsayin babban mai gabatar da jawabi ya biyo bayan cikakken binciken da wani kwamiti na masana da masu nazarin manufofin gwamnati suka gudanar.

Ya ce kwamitin ya yi la’akari da ƙwarewar Musa a harkokin soji, haɗin gwiwar hukumomin tsaro da kuma manufofin tsaron ƙasa. A cewarsa, ana sa ran Ministan zai yi bayani kan alaƙar da ke tsakanin tsaron ƙasa da gudanar da zaɓe cikin ’yanci, adalci da sahihanci.

Ya ce taron zai kuma tattauna barazanar da ka iya kawo cikas ga tsarin zaɓe, ciki har da satar mutane, ’yan bindiga, tsattsauran ra’ayi, hare-haren yanar gizo, yaɗa labaran ƙarya, tashin hankalin siyasa da kai hari kan kayayyakin zaɓe da jami’an zaɓe.

Umar ya bayyana Yilwatda a matsayin gwarzon shekara

Salisu Umar ya bayyana Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, a matsayin babban abin da ya fi jan hankali a bikin, inda ya sanar da shi a matsayin “Blueprint Newspapers Person of the Year.”

Ya ce wannan lambar yabo ce da ake bai wa fitattun ’yan Nijeriya waɗanda suka bayar da gagarumar gudummawa wajen ci gaban ƙasa. A cewarsa, shugabancin Yilwatda na jam’iyyar APC a shekarar da ta gabata ya kasance mai haɗa kan ’yan jam’iyya da samar da sakamako mai kyau. Ya ce Yilwatda ya taimaka wajen ƙarfafa haɗin kan jam’iyya, inganta tsarinta, tabbatar da daidaito da kuma samar da jagoranci a sassa daban-daban na jam’iyyar.

Umar ya taya waɗanda aka karrama murna

Manajan Daraktan ya taya dukkan waɗanda aka karrama murna, ciki har da waɗanda suka halarci bikin da kansu da waɗanda suka aika da wakilai. Ya amince cewa zaɓar waɗanda suka cancanci karramawar daga cikin ɗimbin ’yan Nijeriya da ke ba da gudummawa wajen ci gaban ƙasa ba abu ne mai sauƙi ba.

“Zaɓar waɗanda suka cancanci lambar yabon aiki ne mai wahala. Ya yi kama da ƙoƙarin nemo allura a cikin tarin ciyawa,” inji shi.

Ya ce kwamitin zaɓen ya samar da jerin mutanen da suka cancanci karramawa daga fannoni daban-daban, bisa irin gudummawar da suke bayarwa wajen gina ƙasa da bunƙasa tattalin arziki. Ya ce: “Muna taya ku duka murna, kuma muna fatan karramawar da aka yi muku a yau za ta zama ƙarin ƙwarin gwiwa gare ku wajen yin abubuwa masu yawa a fannonin da kuke gudanar da ayyukanku.”

Blueprint ta faɗaɗa zuwa gidan rediyo

Alhaji Salisu ya kuma sanar da faɗaɗa ayyukan Blueprint Newspapers zuwa fannin kafofin yaɗa labarai na zamani, inda aka ƙaddamar da Blueprint Radio. Ya ce gidan rediyon, mai amfani da mitar FM 105.3, ya fara aiki a zangon farko na shekarar, kuma a halin yanzu yana watsa shirye-shirye da harshen Hausa.

Ya ce matakin ya biyo bayan ci gaban da jaridar ta samu a harkar buga jaridu da kuma burinta na faɗaɗa isar da saƙonta ta hanyoyin sadarwar zamani. Umar ya yaba wa shugabannin Blueprint da kwamitin bayar da kyaututtuka

Manajan Daraktan ya yaba wa tawagar gudanarwar Blueprint bisa gudummawar da suke bayarwa wajen bunƙasa harkokin kamfanin da tabbatar da gudanar da ayyukansa cikin nasara duk da ƙalubalen da masana’antar yaɗa labarai ke fuskanta. Ya kuma yaba wa Kwamitin Kyaututtukan Blueprint, wanda Hajiya Zainab Suleiman-Okino ke jagoranta, bisa ƙoƙarin da suka yi wajen shirya bikin. Ya ce kwamitin ya yi aiki tuƙuru wajen shirya taron, yana mai godiya ga mambobinsa bisa abin da ya bayyana a matsayin gagarumin shiri.

Yadda Gwamna Dauda na Zamfara ya yi zarra a cikin gwamnoni

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya samu lambar yabo ta jaridar Blueprint ta 2026 kan Ingantaccen Gudanar da Dukiyar Al’umma da Gaskiya, saboda yadda aka yaba da salon tafiyar da albarkatun gwamnati da kuma ƙoƙarinsa na tabbatar da gaskiya da riƙon amana a mulkin jihar.

Gwamnan ya karɓi kyautar ne ranar Talata a bikin lakca ta shekara-shekara da bayar da lambobin yabo na Kamfanin Jaridun Blueprint karo na takwas, wanda aka gudanar a Cibiyar Taro ta Ƙasa da ƙasa ta Bola Ahmed Tinubu a Abuja.

Taken taron na bana shi ne: “ƙalubalen Tsaro da Amincin Zaɓen Nijeriya na 2027.” Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar da ranar 18 ga Agusta, 2026.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Lawal ya nuna godiyarsa ga mahukuntan jaridun Blueprint, tare da alƙawarin ƙara himma wajen cika manufar gwamnatinsa ta ceto da sake gina Jihar Zamfara.

Ya ce, lambar yabon ta nuna cewa kafafen yaca labarai da sauran ’yan Nijeriya da ke wajen Zamfara suna lura da irin ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi wajen dawo da jihar kan turbar ci gaba.

Gwamnan ya ce, a cikin shekaru uku da gwamnatinsa ta yi, an samu nasarori a fannoni da suka haɗa da tsaro, ilimi, kiwon lafiya, tattalin arziki, bunƙasa jarin ɗan Adam da samar da ababen more rayuwa, yana mai cewa gaskiya da buɗaɗɗen shugabanci ne suka taimaka wajen cimma waɗannan nasarori.

A cewar jaridar Blueprint, an bai wa Gwamna Lawal kyautar ne saboda tsantsar kula da albarkatun gwamnati, riƙon amana wajen harkokin kuɗaɗen gwamnati da kuma ƙoƙarin inganta tsarin mulki mai gaskiya a Zamfara.

Jaridar ta ce, kyautar ta jaddada muhimmancin gudanar da dukiyar jama’a cikin gaskiya da sanin ya kamata, tare da nuna alaƙar da ke tsakanin tsauraran matakan kula da kuɗin gwamnati da samun ci gaba mai amfani ga kowa.

Manajan Daraktan Kamfanin jaridun Blueprint da Manhaja, Salisu Umar, ya bayyana Gwamna Lawal a matsayin mutum da ya haɗa ƙwarewar aiki da hidimar al’umma. Umar ya ce, ƙwarewar gwamnan a fannonin diflomasiyya, harkar banki da siyasa ta ba shi cikakkiyar fahimta kan shugabanci, sarrafa kuɗaɗen gwamnati da jagorancin hukumomi. Ya ce, tun bayan hawansa kujerar gwamnan Zamfara, Lawal ya ci gaba da aiwatar da manufofin da suka shafi dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali, inganta ababen more rayuwa, ƙarfafa hukumomin gwamnati da samar da damammaki ga bunƙasar tattalin arziki.

A cewar jaridar, gwamnatin Lawal ta mayar da hankali wajen ƙarfafa tsarin kula da kuɗaɗen gwamnati, tabbatar da riƙon amana a ɓangaren gwamnati da kuma tabbatar da cewa ana karkatar da dukiyar jama’a zuwa ayyukan da za su samar da sakamako mai auna tasiri ga al’ummar Zamfara.

Jaridar Blueprint ta ce, Gwamna Lawal ya kasance yana jaddada muhimmancin kasafin kuɗi mai nagarta, ingantaccen samar da ayyukan gwamnati da kuma taka-tsantsan wajen sarrafa kuɗaɗen jihar a matsayin ginshiƙan ci gaba mai ɗorewa. Jaridar ta kuma ce gwamnatin ta tallafa wa wasu shirye-shirye da suka shafi inganta ayyukan tsaro, kare al’ummomin karkara da samar da yanayin da zai ba mutanen da suka rasa matsugunansu damar komawa gidajensu tare da sake gudanar da harkokin rayuwa da sana’o’insu.

A ɓangaren ababen more rayuwa kuwa, jaridar ta ce gwamnatin Lawal ta ba da muhimmanci sosai wajen sake gina ababen more rayuwa a faɗin jihar. Ta ce, gwamnati ta gudanar da ayyukan gyaran tituna da gina sababbi, inganta gine-ginen gwamnati da zuba jari a wasu muhimman ayyukan more rayuwa da aka tsara domin bunƙasa kasuwanci, sauƙaƙa zirga-zirga da inganta damar jama’a na samun muhimman ayyukan gwamnati.

A cewar jaridar, waɗannan ayyuka na da nufin sake haɗa al’ummomi, sauƙaƙa harkokin tattalin arziki da kuma tabbatar da ci gaba mai daidaito tsakanin birane da yankunan karkara.

Jaridar ta ƙara da cewa gwamnatin Lawal ta fahimci cewa ilimi na daga cikin muhimman hanyoyin rage talauci da samar da damar samun makoma mai kyau ga al’ummomi masu zuwa. Haka kuma, ta ce gwamnatinsa ta aiwatar da wasu sauye-sauye da nufin ƙarfafa harkokin ba da kiwon lafiya a faɗin Jihar Zamfara.

By ukarofi

Leave a Reply