Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya ce matakin Peter Obi na ficewa daga jam’iyyar ADC ya kawo ƙarshen damar da yake da ita ta lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Fayose ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na TVC News, inda ya ce ‘yan adawa sun raunana damar da suke da ita ta kayar da jam’iyyar APC, bayan da suka rabu suka bi hanyoyi daban-daban.
Ya ce a lokacin da manyan ‘yan adawar suka kasance cikin haɗin gwiwar ADC, suna da damar yin gagarumar hamayya da APC, amma ficewar Obi daga ƙawancen ta sauya lamarin.
Sai dai Fayose ya yaba wa Peter Obi, inda ya bayyana shi a matsayin ɗan Nijeriya nagari wanda ya bayar da gudummawa wajen ƙoƙarin inganta ƙasar.
Ya ce matsalar ita ce rashin haɗin kan ‘yan adawa, wanda a cewarsa zai ci gaba da rage musu damar kayar da APC a zaɓen 2027.
Ya yi hasashen cewa Tinubu zai iya samun kusan ƙuri’a miliyan huɗu daga yankin, bisa la’akari da yanayin zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Ya yi zargin cewa magoya bayan jam’iyyu daban-daban, ciki har da APC, PDP da Accord Party, na iya kasancewa cikin irin wannan dabi’a.
Ya ce matsalar magudin zaɓe da sayen ƙuri’a matsala ce da ta shafi tsarin zaɓe baki ɗaya, kuma tana buƙatar haɗin gwiwar jam’iyyu, ‘yan takara, hukumomin tsaro, INEC da masu zaɓe domin magance ta.
