‘Yan bindiga sun sace uwa da ɗa bayan halaka ɗan bijilante a Kaduna

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu ‘yan bindiga sun halaka ɗan bijilante da kuma sace wata mata tare da ɗanta yayin wani hari da suka ƙaddamar a ƙauyen Kyauta da ke yankin Millennium City a Jihar Kaduna.

Ɗan bijilanten mai suna Mustapha Baba, ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da maharan suka harbe shi, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa yayin da yake karɓar magani a Asibitin Barau Dikko Specialist da ke Kaduna.

Ɗan uwansa Yuzuf Baba ne ya tabbatar da faruwar al’amarin a wani rubutu da ya wallafa a shafin Soshiyal Mediya, inda ya ce harin ya auku ne a ranar Laraba cikin dare. A cewarsa, maharan sun afka wa mutane ne a wani gida da ke kusa da Masallacin Mai-Rago, inda suka nemi ganin mai gidan. Kasancewar ba su same shi ba sai suka yi awon-gaba da mata da ɗansa.

Wannan shi ne hari na kwanan nan daga cikin jerin hare-hare da suke yawan aukuwa a yankin da ma wasu wurare a Millennium City.

A wani ɓangare kuwa, an sace wasu mazauna su biyar a yankin Police Estate da ke Baban Saura a daidai lokacin da ‘yan yankin suka yawaita kira ga gwamnati na a ƙarfafa matakan tsaro da inganta titinan Millennium City.

A cewar wani mazaunin yankin mai suna Alhaji Abu Mohammed, ya dace gwamnati ta ƙoƙarta wajen kammala aikin titin Eastern Bypass ciki har da gada, saboda rashin kyan hanyoyin yankin na haifar da cikas ga ƙoƙarin jami’an tsaro na magance matsalolin barazanar tsaro a yankin.

By Babaji

Leave a Reply