Na hannun daman Trump ya faɗi a zaɓen fidda gwanin takarar gwamnan Florida

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Yayin da masu zaɓe suka shirya maye gurbin Gwamna Ron DeSantis mai barin gado, ‘yan jam’iyyar Republican sun zaɓi na hannun daman Shugaban Donald Trump, yayin da Democrat suka zaɓi wani ɗan takara daban da ya sauya jam’iyya ya bar tafiyar GOP (Republican) saboda shugaban ƙasar.

Saidai kuma masu goyon bayan Democrat sun sake nuna ƙarfinsu na cigaba da samun karɓuwa bayan Rep. Angie Nixon ya lashe zaɓen fidda gwanin ɗan takarar sanata. Amma biyu daga cikin ‘ya’yan majalisa na jam’iyyar da suka tsaya takara a karon fari a sababbin gundumomi sun tsallake rijiya da baya.

Haka ma Rep. Cory Mills, wanda ɗan majalisa ne na Republican, wanda ke fuskantar bincike kan ƙwarewa a matakai daban-daban, ya rasa kujerarsa a ranar Talata, inda wani tsohon ɗan jarida da ya samu goyon bayan mambobin GOP na tawagar majalisar dokokin ƙasar, ya doke shi.

A wani ɓangare kuwa, CNN ta ruwaito cewa, mambobin GOP, Sanata Dan Sullivan da tsohuwar ‘yar majalisa ta Democrat, Mary Peltola sun tsallake zuwa zagayen babban zaɓe domin neman kujerar sanatan Alaska. Ana ganin Democrat za ta amfana matuƙar Dan Sullivan ya lashe zaɓen na Nuwamba.

A zaɓen gwamnan Florida kuwa, Trump yana goyon bayan Byron Donald, yayin da Democrats ta tsayar da tsohon ɗan majalisa Rep. David Jolly, wanda ya fice daga Republican a 2018 kuma ya koma ɗan Democrat a hukumance a 2025.

By Babaji

Leave a Reply