Adadin ‘yan Nijeriya da ke fuskantar barazanar kora a Amurka ya kai 157 bayan ƙasar ta ƙara 24

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ma’aikatar Harkokin Tsaron Cikin Gida ta Amurka (DHS) ta sanar da ƙara wasu ‘yan Nijeriya guda 24 a jaddawalin waɗanda take shirin kora daga ƙasarta, matakin da ya kai adadin ‘yan Nijeriyar zuwa 157 a rajistarta mai suna “Worst of the Worst”. DHS ta bayyana haka ne a shafinta na Intanet, inda ta ce sababbin ‘yan Nijeriyar da aka ƙara an kama su ne bisa laifukan damfara, sauya akalar kuɗaɗe, ta’ammali da ƙwayoyi, satar shaidar ƙasa da muzguna wa ‘ya’ya.

Wallafar ma’aikatar ya nuna yadda hukumomin Amurka da suka haɗa da na Shige-da-Fice da Kwastam suke kama ‘yan ƙasashen waje bisa manyan laifuka da fuskantar kora daga ƙasar. Jaddawalin, wanda ya bayyana mutanen a matsayin ‘yan Nijeriya, ya kuma bayyana cewa an ɗauki matakin ne bisa zargin su da laifukan damfara ta saƙo, damfarar Intanet, sojan gona, ayyukan bogi, cin zarafi da laifukan da suka shafi makamai.

Daga ‘yan jaddawalin akwa Emmanuel Omowaiye, da aka kama a yankin Richmond na Jihar Texas, bisa laifin saƙon damfara; Laurene Onwuka a Chantilly, da ke Virginia, kan sojan gona; da Olusegun Shonekan da aka cafke a Newark da ke New Jersey, kan damfara ta Intanet. Sauran sun haɗa da Olusegun Olaseni a Greencastle, Indiana, kan siyar da maganin ƙara kuzari na ‘amphetamine’; Peter Ude a Atlanta, Georgia kan damfarar Intanet; da Newton Jemide da aka kama a Fort Dix da ke New Jersey, kan damfara ta Intanet, makirci da kuma damfara ta aike saƙo.

Haka kuma, a cikin jaddawalin akwai Shedrack Umukoro da aka cafke a Yazoo City, Mississippi, kan badaƙalar kuɗaɗe; Olasoji Akinbode Kearny, New Jersey kan sojan gona da kuma Oluwatosin Afolabi a yankin Conroe na Texas kan damfara. Alameen Adetunji Tokosi a Chicago, Illinois kan mallakar tabar wiwi, da Joshua Ipoade a Atlanta, Georgia kan damfarar Intanet. Sannan an kama wani ɗan Nijeriya, Michael Orji a Oxford, Wisconsin kan laifukan makamai, damfara, satar shaidar ƙasa, damfarar Intanet, ƙaryar zama ɗan ƙasa da kuma badaƙalar kuɗaɗe.

Zango na biyu na ‘yan Nijeriyar sune Ahmadu Apooyin a Baltimore, Maryland, kan laifukan ta’amali da hodar Ibilis; Teslim Kiriji a Yazoo City, Mississippi, kan sauya akalar kuɗaɗe; da Onomen Uduebor a Seattle, Washington kan satar shaidar ɗan ƙasa. Akwai kuma Charles Ochi da Daniel Eta a White Deer, Pennsylvania, kan sauya akalar kuɗaɗe da damfarar Intanet.

Ifeanyi Ibennah a Tampa, Florida, kan muzguna wa yaro, yayin da Kazeem Runsewe aka kama shi a Thomson, Illinois da Fatiu Lawal a Lompoc, California kan damfara a Intanet. Jaddawalin ya kuma ƙunshi Justin Akubueze a Orem, Utah akan sauya akalar kuɗaɗe; Moyinoluwaseun Okeowo a Orlando, Florida kan sata, ayyukan bogi da ɓoye kayan sata; Babajide Oluwaseun Faseyi a Alden, New York kan cin zarafi; da kuma Bright Eigbedion a Lompoc, California kan sauya akalar kuɗaɗe.

A cewar ma’aikatar, wannan aiki ƙoƙarin ne na gwamnatin Shugaba Donald Trump ta korar ‘yan ƙasashen waje da aka samu da hannu a manyan laifuka daga ƙasar. Saidai, ba a bayyana lokacin da za a fitar da ‘yan Nijeriyar daga ƙasar ba a lokacin haɗa wannan rahoto.

By Babaji

Leave a Reply