
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sabon kociyan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United, Mauricio Pochettino ya fuskanci babban ƙalubale a wasansa na farko bayan ƙungiyar Liverpool ta lallasa su da ci 4 da 0 a filin wasan Anfield, a ranar 22 ga Nuwamba a wasa na 11 na gasar Premier League ta ƙasar Ingila ta 2026/27.
Ɗan Ajantinan a wasansa na farkon ya gamu da matsala ne bayan fara wasan, inda a minti na takwas aka bai wa ɗan wasansa L. Yoro jan kati, matakin da ya bai wa Liverpool damar samun zura ƙwallo biyu a minti 13 na farkon wasan da kuma ƙara wasu ƙwallo biyu bayan koma wa hutun rabin lokaci.
Wannan rashin nasara ya haifar da cikas ga Pochettino, wanda ya zo da nufin dawo da martabar United, wadda a yanzu take a mataki na 19 a teburin frimiyar da maki takwas kacal daga wasanni 11 da ta buga. A gefe guda, Liverpool ta koma mataki na huɗu da maki 21, wato maki bakwai tsakaninta da Arsenal wadda ita ce ta ɗaya a teburin.
Ita ma Brighton and Hove Albion da ke mataki na biyu da maki 22 a teburin da fuskanci tsaiko a matakin biyo bayan doke ta da Hull City ta yi da ci 2 da 0 ana dab da tashi a wasan, yayin da Bournemouth, Tottenham Hotspur da Coventry City suka samu muhimman nasarori a gasar.
Manchester City ta su koci Enzo Marresca ta kasa doke Fulham a filin wasa na Etihad bayan an tashi wasa 1 da 1 a ranar Asabar, kamar yadda ita mai kofin, Arsenal ta tashi 2 da 2 tsakaninta da Newcastle.
Cikakken sakamakon wasanni na 11
Asabar, 21 ga Nuwamba, 2026
Manchester City vs Fulham 1-1
Aston Villa vs Sunderland 0-0
Bournemouth vs Nottingham Forest 2-0
Chelsea vs Leeds United 1-4
Coventry City vs Crystal Palace 3-2
Tottenham Hotspur vs Ipswich Town 2-0
Newcastle United vs Arsenal 2-2
Lahadi, 22 ga Nuwamba, 2026
Hull City vs Brighton 2-0
Liverpool vs Manchester United 4-0
Litinin, 23 ga Nuwamba, 2026
Brentford vs Everton 4-0
