Instagram ta cire bidiyon dambarwar Sarkin Daura da Baturiya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Litinin, 23 ga Nuwamba, 2026 dandalin Instagram ya cire bidiyon da ya karaɗe kafafen sada zumunta wanda wata baturiya mai yawon buɗe ta ɗora, inda a ciki ta zargi Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk da yunƙurin cin zarafinta a lokacin da kai ziyara a fadarsa da ke Jihar Katsina.

Wannan al’amari ya haifar da sabon cece-kuce, inda ‘yar yawon buɗe ido ta tirje akan cewa ba ta goge bidiyon ba, amma ta ce ta yiwa an cire shi ne sakamakon yawan kai ƙorafi da masu amfani da manhajar da dama suka yi. Matar mai suna Mirka Czee kuma take amfani da sunan @beduinqa, ta buƙaci a yi nazari akan matakin dandalin, inda ta bayyana rashin tabbas kan yadda tsawon lokacin ɗaukaka ƙarar zai kai.

An cire bidiyon ne sakamakon yadda al’amarin ya janyo hankalin jama’a kan zarge-zargen, wanda ya sa aka yi kira da a gaggauta gudanar da bincike mai zaman kansa a kai da bayar da amsa a hukumance daga ɓangaren hukumomin da al’amarin ya shafa.

Matar, wadda aka haifa a ƙasar Czech Republic, ta ce ta yawata a sassan Nijeriya ciki har da Oron, Calabar, Ibadan, Benin City, Lagos, Abeokuta, Osogbo, Ilorin, Abuja, Jos, Bauchi, Dutse, Kano, Zaria, Katsina da kuma Daura. A cewarta, tana tafiye-tafiyen nata ne a motocin ‘yan kasuwa kuma tana tattaunawa da mazauna domin gane yadda al’adu da bambance-bambancen Nijeriya suke, inda ta ƙara da cewa ta haɗu da mutanen kirki masu taimako da karrama mutane.

Sannan, ta ce ta gana da wasu sarakuna a Nijeriya da bayyana hakan a matsayin abin da aka yi bisa girmamawa. Kazalika, ta yi zargin cewa a lokacin da ta je fadar ta Daura, an nuna mata ababen tarihi a wasu wurare ciki har da kai ta wajen da ta haye kan doki da nufin nishaɗi. A cewarta, daga bisani an mayar da ita wajen Sarkin, saidai an bar ta ita kaɗai a wani babban ɗaki daga ita sai sarkin.

Ta yi zargin cewa, sarkin ya buƙaci da ta zauna a kusa da shi akan wata kujera, inda ya riƙe hannunta ya fara wasa da shi, lamarin da ya sa ta fara jin ta a halin takura. Czee ta ce, a lokacin ne ta sauke tabaranta mai ɗauke da kyamara da sanya shi a halin naɗar abin da ke faruwa a daidai lokacin da ta yi ƙoƙarin jan hankalinsa don cigaba da hirar tsakaninsu.

Har ila yau, ta yi zargin cewa sarkin daga bisani sai ya rungume ta ya kuma sumbace ta a kumatu yayin da suka miƙe tsaye kafin ya taɓa mata mama ba tare da amincewarta ba. Ta bayyana cewa hakan ya girgiza ta, inda ta cigaba da faɗa masa cewa ya daina taɓa ta.

By Babaji

Leave a Reply