Tinubu ya ƙara jihohin da zai je kamfen daga 12 zuwa 19

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya faɗaɗa jadawalin rangadin gangamin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2027, inda ya ƙara yawan jihohin da yake shirin ziyarta daga 12 zuwa 19, baya ga Babban Birnin Tarayya Abuja.

Blueprint Manhaja  ta rawaito cewa sabon jadawalin ya nuna cewa shugaban ƙasar zai ƙara shiga cikin gangamin neman goyon bayan jam’iyyar APC a faɗin ƙasar, inda ake sa ran zai halarci tarukan yaƙin neman zaɓe guda 20.

Sabon jadawalin ya ƙunshi lokacin daga ranar 24 ga Oktoba, 2026, zuwa 13 ga Janairu, 2027.

Daga cikin jihohin da aka ƙara cikin jadawalin gangamin shugaban ƙasar akwai Katsina, Taraba, Zamfara, Imo da Kwara. Haka kuma, an saka Akwa Ibom, Jigawa da Kebbi bayan Tinubu ya halarci tarukan gangami a waɗannan jihohi a baya-bayan nan.

Shugaban ƙasar ya riga ya kai gangamin neman zaɓe zuwa wasu wurare da ba sa cikin jadawalin farko, lamarin da ke nuna sauyin tsarin da aka fara tanada, inda aka shirya shugabannin APC za su wakilce shi a wasu tarukan jihohi.

A ranar 6 ga Nuwamba, Tinubu ya halarci gangamin jam’iyyar a Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom, inda ya kuma ƙaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin Gwamna Umo Eno ta gudanar.

Daga nan ya halarci gangamin neman zaɓe a Fatakwal, Jihar Rivers, a ranar 7 ga Nuwamba, kafin ya halarci tarukan gangami a Dutse, Jihar Jigawa, ranar 10 ga Nuwamba, da kuma Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, ranar 17 ga Nuwamba.

A ƙarƙashin sabon jadawalin, ana sa ran shugaban ƙasar zai halarci gangami a Katsina ranar 2 ga Disamba, Kano ranar 17 ga Disamba, Jalingo ranar 19 ga Disamba, sannan Abuja ranar 21 ga Disamba.

Sauran tarukan da aka tsara sun haɗa da na Gusau, Jihar Zamfara, ranar 28 ga Disamba, da Owerri, Jihar Imo, ranar 30 ga Disamba.

Ana sa ran Tinubu zai ci gaba da ayyukan gangaminsa a sabuwar shekara, inda zai fara da Yola, Jihar Adamawa, ranar 4 ga Janairu; Sokoto ranar 5 ga Janairu; da Ilorin, Jihar Kwara, ranar 8 ga Janairu.

Daga nan shugaban ƙasar zai ziyarci Asaba, Jihar Delta, ranar 11 ga Janairu, kafin ya kammala gangamin da babban taro a Legas ranar 13 ga Janairu.

Sabon jadawalin ya kuma ƙunshi sauye-sauye masu muhimmanci daga tsarin da aka fitar da farko.

Daga cikin sauye-sauyen akwai ɗage gangamin Sokoto daga ranar 5 ga Disamba zuwa 5 ga Janairu, da kuma sauya ranar babban taron kammala gangamin Legas daga 9 zuwa 13 ga Janairu.

An kuma sauya ranar gangamin Bauchi, wanda aka fara tsara gudanarwa a ranar 29 ga Nuwamba, inda aka mayar da shi zuwa 1 ga Disamba. Sai dai sabon jadawalin bai nuna cewa Tinubu zai halarci taron da kansa ba.

Duk da cewa APC ta tsara gudanar da gangami guda 37 a faɗin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, ana sa ran Tinubu zai halarci taruka 20 da kansa, yayin da sauran shugabannin jam’iyyar za su jagoranci sauran tarukan.

Bayanan sabon jadawalin sun nuna cewa Arewa maso Yamma ce ke da mafi yawan jihohin da shugaban ƙasar zai ziyarta, inda aka lissafa guda bakwai: Kaduna, Jigawa, Kebbi, Katsina, Kano, Zamfara da Sokoto.

Arewa maso Gabas da Kudu maso Kudu suna da jihohi uku-uku, yayin da Arewa ta Tsakiya, Kudu maso Yamma da Kudu maso Gabas suke da jihohi biyu-biyu.

Wannan rabon ya nuna cewa Arewa maso Yamma ce za ta fi samun ziyartar shugaban ƙasar a ƙarƙashin sabon jadawalin, duk da cewa an tanadi tarukan gangami a sauran yankunan siyasa na ƙasar.

A baya, Tinubu ya shaida wa mambobin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban ƙasa na APC a Abuja cewa ba zai iya halartar dukkan tarukan gangamin ba, saboda buƙatar daidaita ayyukan neman zaɓe da nauyin gudanar da gwamnati.

Sai dai ya yi alƙawarin ware lokaci domin ganawa kai tsaye da ’yan Nijeriya, yayin da shugabannin jam’iyyar za su kai gangamin zuwa jihohi da ƙananan hukumomi daban-daban.

Jaridar ta rawaito cewa faɗaɗa sabon jadawalin gangamin Tinubu ya zo ne bayan ce-ce-ku-ce da aka yi kan matakin farko na shugaban ƙasar na takaita ziyartar jihohi 12, inda aka bar shugabannin jam’iyyar su wakilce shi a tarukan wasu jihohin.

A ranar 14 ga Oktoba, yayin ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban ƙasa na APC, shugaban ƙasar ya sanar da cewa ba zai halarci dukkan tarukan gangamin ba.

Ya bayyana cewa nauyin gudanar da gwamnati, wajibai na kuɗi da kuma buƙatar jawo hankalin masu zuba jari na dogon lokaci ne suka sa ya yanke shawarar takaita halartar tarukan.

Ya shaida wa mambobin kwamitin cewa: “Don haka, za ku yi haƙuri da ni idan ba zan iya zuwa ko’ina tare da ku ba; muna da kuɗaɗen da za mu biya. Masu bin mu bashin Amurka ba za su jira ba.”

By ukarofi

Leave a Reply