‘Namu ‘ya’yan fa?’, iyayen Borno sun yi wa Tinubu magiya kwana 40 da ceto ‘yan makarantar Oyo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Iyayen ɗaliban makarantar da aka yi awon-gaba da su a Jihar Borno sun yi magiya ga Shugaba Bola Tinubu da ya shiga tsakani domin ceto ‘ya’yansu, inda suka koka kan cewa yayin da aka kai kwana 40 da ceto ɗaliban Jihar Oyo, nasu sun ɗauko hanyar kaiwa kwanaki 100 a hannun masu garkuwa da su.

Manhaja ta ruwaito cewa, iyayen, waɗanda suke cikin alhini, sun yi wannan koke ne a yayin hira da gidan talabijin na News Central, inda suka yi ƙalubale cewa ya aka yi ‘yan Oyo suka shaƙi iskar ‘yanci amma kuma ɗaliban Borno da aka sace su a rana guda har yanzu ba a su dawo cikin iyalansu ba, wanda hakan ya sanya makusantansu cigaba da zama cikin halin rashin tabbas na tsawon lokaci.

Iyayen sun yi wannan magiya ne kai tsaye ga Shugaba Tinubu, inda suka roƙe shi da ya tabbatar da ceto yaran nasu cikin aminci. Sannan, sun zargi gwamnatin da gazawa wajen rashin daidaita darajar rayukan yara a sassan ƙasar.

A cewarsu, rashin tabbas kan sanin halin da ‘ya’yan suke ciki ya sa wasu iyayen sun kamo da hawan jini ta yadda har ta kai ga an ba su gado a asibiti a sanadiyyar ƙunci da suke ciki kan al’amarin.

“Kuma wane laifi ne, mu iyaye, muka yi wa gwamnatin da har muka cancanci wannan uƙuba?”, inji ɗaya daga cikinsu.

A ranar 15 ga watan Mayu, 2026 ne aka yi garkuwa da yaran, rana guda da ‘yan bindiga suka yi awon-gaba da ɗalibai da malamai daga wata makaranta a yankin Oriire da ke Jihar Oyo.

“‘Yata ta cika shekara huɗu a ranar 17 ga Yuli watan da ya gabata. Sannan, wasu na hannun masu garkuwar da ba su kai ‘yar tawa ba,” inji wata uwa.

Kazalika, sun ce har yanzu ba su samu wani labari na samun tabbacin yaran nasu suna cikin ƙoshin lafiya ba, lamarin da ya sa kullum suke cikin zullumi kan ko suna raye kuma a’a.

“Dan Allah muna buƙatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dubi wannan yanayi. Dan Allah ya shiga tsakani kan wannan al’amari a dawo da waɗannan yara. Dan Allah, wannan shi ne kaɗai abin da muke so daga gwamnatin,” kamar yadda suka yi magiya.

By Babaji

Leave a Reply