
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Fadar Shugaban Ƙasa ta caccaki kalaman ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar na cewa zai mayar da tallafin fetur idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban Nijeriya a 2027.
Mai taimaka wa Shugaba Bola Tinubu kan Sadarwa da Wayar da Kan Al’umma, Sunday Dare a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana shirin Atikun a matsayin yunƙurin kwaɗaitar da ‘yan Nijeriya domin su zaɓe shi.
A ‘yan kwanakin nan ne dai ɗan takarar na ADC ya ci alwashin maido da tallafin fetur matuƙar ya lashe zaɓen 2027, wanda gwamnatin Shugaba Tinubu ta cire a farkon mulkinta a shekarar 2023.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya soki tasirin tattali da cire tallafin fetur ya yi a ƙarƙashin mulkin Tinubu, yana mai cewa har yanzu ‘yan Nijeriya ba su ga amfani da hakan ya yi ba daga tsarin.
Saidai, yayin bayar da amsa ga kalaman Turakin Adamawan, Sunday Dare ya yi iƙirarin cewa Atiku bai gamsu da nasarorin da aka samu ba a fannin tattali a Nijeriya ta sanadiyyar gyare-gyaren da Tinubu yake yi. Ya ƙara da cewa, shirin Atiku na dawo da tallafin zai mayar da hannun agogo baya ne na ribar da aka samu ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.
A cewarsa: “Da yardar Allah hakan ba zai faru ba, kuma dukkan mutanen kirki masu kyawawan manufa ba za su amince da kai ba,” inji shi a ƙarshe.
