Daga MUKHTAR YAKUBU
A yanzu haka dai mawaƙiyar yabon Manzon Allah Kuma ‘yar gwagwarmaya Faridat Hussaini Masheliya ta rikide ta zama cikakkiyar marubuciya. Don kuwa a ‘yan kwanakin nan ta fara tallan sabon littafin ta da take shirin fitar da shi a nan da ɗan lokaci mai zuwa.
Littafin mai suna ‘Yar Mulki’ wanda kuma an fassara shi zuwa Turanci, don haka zai fito kala biyu ne na Turanci da kuma na Hausa.
Domin jin abubuwan da littafin ya ƙunsa da dalilin ta na fito da shi, wakilinmu ya tattauna da ita don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance
MANHAJA: Kina shirin fito da wani sabon littafi mai suna ‘Yar Mulki’ wanda na Hausa ne da Turanci. Za mu so ki yi mana bayani dangane da littafin.
FARIDAT MASHELIYA ‘Yar Mulki’ labari ne a kan wata matar aure da ta tsunduma cikin harkan nanaye saboda matsi da kuncin rayuwa, inda ta haɗu da wani shahararren mawaƙin da ya taimaki rayuwarta har ma suka yi auren taƙaitaccen lokaci ba tare da ya san akwai igiyoyin da suka ɗaure ta tamau ba, ya taimaki rayuwarta inda ya nemi daukinta a lokacin da ya shiga cikin wani matsin da yake burin ganin ta zama matarsa ta huɗu. Sai dai lamari ya faskara saboda auren da ke ɗaure a kanta, har tsohuwar bazawarar shi da ya yi wa alƙawarin aure ta bankaɗo sirrin auren nasu. Daga ƙarshe suka yi aure.
Sai dai tsugunne ba ta kare ba, domin ‘Yar mulki ta zame mata ƙarfen kafa. Don haka labari ne da ya ƙunshi cin amana, gwagwarmaya, soyayya da sadaukarwa.
Shi wannan littafin shi ne na farko da kika fara rubutawa?
‘Ƴar Mulki ba shi ne labarina na farko ba sai dai shi ne na farkon da na juya shi da Turanci saboda waɗanda ba sa jin labarin su amfana.
Kin sanar da cewa littafin labarin gaskiya ne. Ko abin ya faru ne a kanki?
A’a bai faru da ni ba sai dai ya faru da wata da take buƙatar a yada shi saboda a faɗa wa duniya illar da wasu maza su ke yi wa mata da yake sanya su su afka bariki ko su shiga harkan nanaye.
Menene dangantakar ki da labarin?
Dangantaka ta da labarin kasancewata marubuciya ce, sannan mawaƙiya wadda take mu’amala da marubuta da mawaƙa har ma da masu shirya fina-finai.
Kin yi suna a waka. Za mu so ki yi mana bayani a kan waƙoƙin ki a yanzu. Kin ja baya ne ko kin ci gaba?
Gaskiya gaba na yi a waka dalilina na cewa haka yanzu fiyayyen halitta Manzon Allah da ahalin gidansa kaɗai nake waƙewa cikin shauƙi da soyayya.
Kuma har na fara fitar da shot-shot na bidiyo wadda ina addu’ar Allah Ya dafa mini ta yadda zan yi bidiyon bege na.
Don haka na ci gaba kamar yadda na fada a baya waƙoƙin suna da yawa amma waɗanda suka zamto sababbi su ne wakata ta Ya Maigida gani na zo godiya Ya rasulillah. Sai ta Annabi Dilmera Hoo Gaya.
Wanne irin buri kike da shi a game da wannan littafin?
Babban burina dangane da wannan kayataccen littafin shi ne in buga shi sannan ya zamo hannunka mai sanda ga maza masu barin mata kara zube sannan ya shiga lungu da saƙo tun da a yanar gizo zan sake shi.
To Madalla na gode, Faridat Hussaini Masheliya.
