2027: Tsohon Sufeto Janar ne zai lashe zaɓen gwamnan Nasarawa, inji Ali Bagio

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Jibrin Ali, wanda akafi sani da Bagio babban mai goyon baya kuma mai tara kuri’u ne na musamman ga qan takarar kujerar gwamnan jihar Nasarawa a karkashin jam’iyyar Social Democratic Party SDP wato tsohon sufeton ‘yan sandan Najeriya alhaji Abubakar Muhammed Adamu inda ya bayyana cewa qan takarar nasa kadai ne zai iya lashe zaben gwamnan dake tafe a jihar.

Bagio ya bayyana haka ne a Lafiya babban birnin jihar yayin tattaunawa na musamman da manema labarai kwanan nan.

Ya musanta zargin cewa babban qan takarar SDP din wanda aka zaba kafin zuwan Abubakar Muhammed Adamu jam’iyyar a yanzu haka ya ki sauka wa tsohon IGP din yana mai cewa zargin karya ne da ake yi domin tayar da rudani a cikin jam’iyyar.

Mai yakin tara kuri’un ga Abubakar Adamu Muhammed ya kuma musanta zargin cewa magoya bayansu ne ke haddasa rigirgimu a jihar inda maimakon haka ya zargi wasu daga cikin masu fada-aji na jam’iyyar All Progressives Congress APC mai mulki da magoya bayanta da zama dalilin rikicin.

Jibrin Ali Bagio ya kuma bai da misali da kayewar APC a zaben gwamnan jihar Osun da aka yi kwanan nan yana mai cewa hakan alama ce ta abin da zai faru a jihar ta Nasarawa a zaben shekarar 2027 dake tafe.

“Rushewar APC a Osun ita ce gwajin da zai nuna abin da zai faru a jihar Nasarawa a 2027 insha-Allah inda jam’iyyar APC mai mulki za ta sha kashi itama a hannun qan takaranmu anan jihar Nasarawa” in ji shi.

Ya kuma yi kira na musamman ga magoya bayan SDP a fadin jihar da su fito da yawan su su kuma tabbatar sun samo katin zaben su na dindindin wato PVC domin su kada kuri’a mai yawa ga Abubakar Mouhammed Adamu a ranar zaben.

Daga karshe sai Ali Bagio har ila yau yayi amfani da damar inda ya tabbatar wa ‘yan jihar baki daya cewa ba za su taba yin nadamar ba da kuri’arsu ga tsohon IGP din ba saboda tarihin sa na yin hidimta wa ‘yan adam baki daya batare da nuna banbancin addini da siyasa ko kabila ba tsawon shekaru da dama inda ya kara da cewa da Abubakar Muhammed Adamu a matsayin jagora a jihar “tabbas makomar jihar ta tabbata,” in ji shi.

Ali Bagio
By Babaji

Leave a Reply