
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kimanin Naira tiriliyan 3 ne Gwamnatin Tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi suka raba a tsakaninsu daga kuɗaɗen asusun tarayya a watan Yuli, 2026, wanda ya zama mafi girma da aka taɓa rabawa a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.
An sanar da haka ne a taron Agusta, 2026 na Kwamitin Asusun Kasafta Kuɗaɗen Tarayya (FAAC) da aka gudanar a Owerri, Babban Birnin Jihar Imo, wanda kuma Ministan Kuɗi da kula da Harkokin Tattali, Taiwo Oyedele ya jagoranta.
Kasafin na watan Yuli ya samu gagarumin ƙari daga tiriliyan N2.551 da aka raba a tsakanin ɓangarorin gwamnatin uku a Yuni, 2026. Idan aka kwatanta da wanda ya gabata, kasafin na yanzu ya samu ƙarin Naira biliyan 456, wanda ke wakiltar kaso 17.9.
A cewar takardar da FAAC ta fitar ta Ofishin Akanta Janar na Ƙasa, Gwamnatin Tarayya ta samu tiriliyan N1.146 daga kuɗin shiga na Yuli da aka tattara. Gwamnatocin jihohi kuwa, sun karɓi jimillar Naira biliyan 943.352, yayin da na ƙananan hukumomi suka samu biliyan N673.649.
Sannan, biliyan N243.478 na wakiltar kaso 13, wanda aka samu daga arziƙin albarkatun ƙasa, kuma an raba su ga jihohin da hakan ya shafa.
Waɗannan kuɗaɗe da aka raba sun nuna muhimmancin kasaftawa a kowane wata da FAAC ke yi ga rassan gwamnatocin musamman na jihohi da ƙananan hukumomi sa suka fi dogara da su wajen biyan albashi, aiwatar da ayyukan ababen more rayuwa da kuma sauran hidindimun al’ummarsu.
FAAC ya ce, an samu ƙarin ne sakamakon hoɓɓasa da aka yi wajen karɓar haraji daga ɓangarorin mai da wasu ababe daban. Jimillar abin da aka samu a Yuli ya kai tiriliyan N4.359 daga tiriliyan N3.700 a Yuni. Wato hakan na wakiltar ƙarin biliyan N658.087 ko kuma kaso 17.8 acikin wata guda.
A cewar kwamitin an samu kuɗaɗen shiga masu yawa daga fannoni da dama ciki har da harajin ribar fetur, harajin ɗanyen mai, harajin kamfanoni, harajin bankuna da dai sauransu, yana mai cewa hakan ya nuna yadda ɓangarorin suke bayar da cikakken haɗin kai da kuma hoɓɓasa wajen karɓowa daga hukumomin tattara haraji a Nijeriya.
