Gwamnan Kano Ahmed Daku

Spread the love

Ahmed Mohammad Daku an haife shi kuma ya yi karatunsa a Katsina. Ya halarci Barewa College daga shekarar 1958 zuwa 1962, sannan ya ci gaba da karatu a Okene Secondary School daga 1962 zuwa 1965.

Aikin Soja:

A shekarar 1967, Ahmed Daku ya shiga Nigerian Defence Academy, inda aka ba shi muƙamin Second Lieutenant shekara guda bayan haka.

Ya shiga yakin basasar Nijeriya a matsayin jagoran dakaru da kwamanda, sannan daga shekarar 1969 zuwa 1972 ya kasance kwamandan batir. An horar da shi a fannin makaman harbo-harbo (Artillery).

Ya halarci Royal School of Artillery da ke Larkhill sau biyu, daga 1970 zuwa 1971, sannan daga 1975 zuwa 1978. Haka kuma, ya halarci Vystrel Academy da ke Tarayyar Soviet (USSR) daga 1974 zuwa 1975. Daga 1976 zuwa 1977 kuma ya halarci School of Artillery a Indiya.

Daga shekarar 1972 zuwa 1974, ya kasance malamin koyar da dabarun amfani da makamai da kuma jami’in ma’aikata a Nigerian Army School of Artillery.

Daga 1974 zuwa 1976, ya zama kwamandan Artillery Regiment na Rundunar Sojin Nijeriya. Daga baya, a shekarar 1976 zuwa 1977, an tura shi hedkwatar Artillery ta Sojin Nijeriya a matsayin Kanal mai kula da harkokin gudanarwa da masauki.

A shekarar 1978 zuwa 1979, ya kasance Mƙaddashin Kwamandan Artillery na runduna.

Ya ci gaba da samun ƙarin girma a aikin soja, inda a shekarar 1980 ya zama kwamandan 42 Field Artillery a Abeokuta. A shekarar 1982, ya zama Kwamandan Medium Regiment na Sojin Nijeriya a Jos.

Daga 1982 zuwa 1985, an tura shi Command and Staff College, Jaji, inda ya kasance malami mai koyarwa a babban mataki.

A shekarar 1985, an ƙara masa girma zuwa matsayin Brigade Commander na 31 Field Artillery Brigade da ke Abeokuta. A wannan matsayi ne ya taka muhimmiyar rawa a juyin mulkin ranar 27 ga Agusta 1985, wanda ya kawo Janar Ibrahim Babangida kan mulki.

Gwamnan Soja na Jihar Kano:

Bayan juyin mulkin, an naɗa Ahmed Daku a matsayin Gwamnan Soja na Jihar Kano.

Ya riƙe wannan muƙami daga Agusta 1985 zuwa Disamba 1987.

A watan Disamba 1987, an sauya shi zuwa Jihar Sokoto, inda ya zama Gwamnan Soja na Jihar Sokoto daga Disamba 1987 zuwa Agusta 1990.

Bayan Aikin Gwamna:

Daga baya, Ahmed Daku ya zama General Officer Commanding (GOC) na 3rd Armoured Division. An sauke shi daga wannan matsayi a watan Satumba 1993, a lokacin rikice-rikicen cikin gida da suka kai ga Janar Sani Abacha ya karɓi mulki.

Daga bisani, ya yi ritaya daga aikin soja, sannan ya koma garinsu na Katsina.

A shekarar 2002, ya jagoranci Directorate of Pilgrims Affairs, hukumar da ke kula da harkokin aikin Hajji.

A shekarar 2003, ya tsaya takarar neman zama Gwamnan Jihar Katsina, amma ya sha kaye a hannun gwamnan da ke kan mulki a lokacin, Umaru Yar’Adua.

A watan Agusta 2009, Ahmed Daku ya bayyana cewa rashin da’a da tarbiyya na daga cikin manyan matsalolin Nijeriya. Ya kuma bayyana cewa ilimi shi ne mafita mafi muhimmanci wajen dawo da martabar Nijeriya da ta ɓata.

By ukarofi

Leave a Reply