
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Akwai yiwuwar dilolin harkar motoci a Abuja su fuskanci ƙalubale yayin da Ministan Abuja, Nyesom Wike ya umarci a gaggauta dakatar da amfani da filayen shaƙatawa a faɗin babban birnin a matsayin wuraren dillanci ko siyasar da motoci.
Rahotanni sun bayyana cewa, umarnin na Wike wani ɓangare ne na ƙoƙarin Hukumar Gudanarwar Birnin (FCTA), na warware matsalolin barazanar ambaliya da ke fuskanta a sassan birnin a wannan daminar.
A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’ar ministan, Lere Olayinka ya fitar wa manema labarai, Wike ya koka kan yadda aka mayar da filayen da aka ware don shaƙatawa a birnin ciki har da Millennium Park da wasu sanannun wurare suka zama wajen dillancin mota. Saboda haka ne ministan ya bayar da umarnin cewa wajibi ne a gaggauta daina amfani da su da irin waɗannan manufa.
Haka kuma, Wike ya umarci a rufe dukkan wuraren shaƙatawa da aka mayar da wajen yin wasu harkoki domin tabbatar da biyayya ga umarnin nasa.
Wannan ci-gaba wani ɓangare ne na FCTA na magance matsalolin da suka haifar da ambaliya a sassan Abuja da kuma tabbatar da cewa ana amfani da wuraren bisa abin da aka samar da su a kai.
Bugu da ƙari, an kafa kwamitin jami’an sanya ido don tabbatar da aiwatar da umarnin ministan da kuma biyayya ga dilolin mota da wasu mutane masu amfani da ire-iren wurare wajen wasu hidimomi. Kazalika, ministan ya bayar da umarnin a fara binciken ma’aikatan da suke bada izini ta haramtattun hanyoyi ga wasu domin yin wata harka a ire-iren wuraren.
