Gwamnatin Tinubu ta faɗi yadda aka sarrafa kuɗaɗe bayan tara tiriliyan N15.8 daga tallafin fetur da sauye-sauyen canjin kuɗi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ce cire tallafin fetur da samar da tsari guda na kasuwar canjin kuɗaɗen ƙasashen waje sun tara mata jimillar Naira tiriliyan 15.8 da ƙarin albarkatu ga ƙasa daga watan Yunin 2023 zuwa Disambar 2025, inda jihohi da ƙananan hukumomi suka samu kaso mafi tsoka.

Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya ta ce kuɗaɗen da aka samu daga cire tallafi bai shiga sahun asusun tarayya ba a ware, wato “subsidy savings”, saidai an bayyana tasirinsa ta kuɗaɗen shiga da aka karɓa sakamakon sauye-sauye a canjin kuɗi da waɗanda aka samu sanadiyyar tasirin cire tallafin.

Ministan Kuɗi da Harkokin Tattali, Taiwo Oyedele ne ya bayyana haka a yau Laraba yayin wani taron manema labarai kan nasarorin da Nijeriya ta samu ta gyare-gyaren da take yi mai taken “The Benefits, Costs and Harm Prevented”, wato Riba, Farashi da Kariya ga Cutarwa.

Wannan warwara ga amsar tambayar da ake yi wa Gwamnatin Tarayya tun bayan sanar da cire tallafin fetur da Shugaba Bola Tinubu ya yi a watan Mayu, 2023 ta cewa: ina kuɗaɗen suka tafi?

A cewar Oyedele, an tura Naira tiriliyan 15.8 ga Asusun Tarayya a ƙarƙashin wani take na musamman da aka bayyana da “subsidy savings”, wato kuɗin da aka tara na tallafi a dunƙule. Ya bayyana cewa, tasirin matakin cire tallafin fetur da sauye-sauyen canjin kuɗi sun taimaka wajen ɗaga darajar Naira daga kuɗaɗe da aka tara wa ƙasa.

Da yake tsokaci kan inda kuɗaɗe suke zuwa, ministan ya ce: “Mutane da dama suna cewa, ‘Ina kuɗaɗen tallafi?’ Haƙiƙanin gaskiya, babu wani sashe a Asusun Tarayya da aka ayyana da ‘subsidy savings'”.

Oyedele ya ƙara da cewa, tasirin waɗannan gyare-gyare suna yiwuwa ne ta kuɗaɗe masu yawa da ake samu na harajin da hukumomin gwamnati suke tattarawa, musamman a sauyin canjin kuɗi da ke ƙara ɗaga darajar Naira daga harajin Dala da ake karɓa.

By Babaji

Leave a Reply