Majalisar dokokin Nasarawa ta tantance sabbin kwamishinoni da Gwamna Sule ya naɗa

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta tantance tare da tabbatar da sabbin kwamishinoni takwas da gwamnan jihar Injiniya Abdullahi Sule ya gabatar ma ta domin a naɗa su cikin majalisar zartarwa ta jihar.

Shugaban majalisar dokokin Rt. Hon. Dr. Danladi Jatau ne ya bayyana haka yau Laraba yayin zaman majalisar a Lafiya bayan an yi tantancewar ga waɗanda aka zaɓa.

Shugaban bayan ya taya su murna kan wannan naɗin da ya cancanta ya kuma buƙace su riƙa aiki da gaskiya da riƙon amana bayan an rantsar da su.

Wakilin mu a jihar ya kuma ruwaito cewa waɗanda aka tabbatar din sun haɗa da:

  1. Muhammad Habeeb Nagogo – Ƙaramar hukumar Wamba
  2. Ahmed Yakubu Mohammed – Karamar hukumar Lafia
  3. Hon. Mohammed Baba Shehu – Karamar hukumar Keffi
  4. Hon. Mohammed Iyimoga Oyigye- Ƙaramar hukumar Obi
  5. Adamu Rabecca Kpadji – Karamar hukumar Wamba
  6. Nawani Aboki – Karamar hukumar Doma
  7. Jibril Abdullahi Ibrahim, FCNA – Karamar hukumar Nasarawa
  8. Ashefo Daniel Paul Ph.D- Karamar hukumar Lafia.

Shugaban ya umarci sakataren majalisar da ya isar ƙudurin in majalisar ga gwamna Abdullahi Sule domin cigaba da mataki na gaba.

Tun farko dai a yayin tantancewar shugaban ‘yan majalisar masu rinjaye Hon. Suleiman Yakubu Azara ne ya gabatar da ƙudirin tantance kwamishinonin inda shi kuma shugaban ‘yan majalisar na jam’iyyar adawa wato marasa rinjayi Hon. Luka Iliya Zhekaba ya mara wa ƙudirin baya.

Idan za a a iya tunawa a ranar 5 ga watan Agusta nan ne na 2026 shugaba Jatau ya bayyana sunayen sabbin kwamishinonin da Gwamna Sule ya gabatar wa majalisar don tantancewar.

A wani labarin kuma makamancin haka majalisar ta kuma zartar da wata dokar kafa kwalejin kiwon dabbobi da fasahar noma ta Obi hedikwatar ƙaramar hukumar Obi a jihar don karatu na farko.

Dokar da ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Obi Dr. Ibrahim Peter Akwe kuma shugaban kwamitin noma na majalisar ne ya ɗauki nauyinta.

Da yake gabatar da ƙudirin Hon. Akwe ya ce wannan cibiya da aka tsara za ta bunƙasa kiwon dabbobi da samar da ayyukan yi da kuma inganta harkar noma a jihar. Hon. Esson Mairiga ne ya mara masa baya.

Bayan karatun shugaban majalisar Dr. Danladi Jatau ya sa ranar 25 ga watan Agusta 2026 domin karatu na biyu a kan dokar.

By ukarofi

Leave a Reply