
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Zartarwar ta Tarayya (FEC) ta ce ta amince da sakin kuɗaɗen da Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta ƙwato ga fannin ilimi ta hanyar sanya su a Asusun bayar da Lamunin Karatu na Ƙasa, NELFUND.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa ne ya bayyana haka jim-kaɗan bayan zaman da FEC ta gudanar a ranar Laraba a Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja, inda ya ce za a sanya kuɗaɗen ne a asusun NELFUND domin ƙarfafa masa wajen sauke nauyin da aka ɗora masa na bai wa ɗalibai aron kuɗin karatu da ke cigaba da faɗaɗa.
Ministan ya ƙara da cewa, FEC ta kuma umarci Antoni Janar na Ƙasa da ya haɗa hannu da Ma’aikatar Ilimi wajen gudanar da ayyukan da za su tabbatar da aiwatar da matakin na tare da jinkiri ba.
Haka kuma, yayin yaba wa hange da sadaukarwar Tinubu ga ilimi, Alausa ya bayyana cewa, kuɗaɗen waɗanda a halin yanzu suna ƙarƙashin shari’a, ba za a iya taɓa su ba har sai an warware dukkan wata matsala akansu.
Kazalika, ya ce FEC ta kuma amince da ƙarin wasu kuɗaɗe ga NELFUND domin ƙara masa ƙarfi yayin gudanar da harkokinsa ciki har waɗanda aka samu daga ‘Capital Market Trust Fund’ da ‘Dormant Account Trust Fund’.
