Rundunar ‘yan sanda ta bada umarnin bincike kan bidiyon zargin jami’anta suna karɓar na goro a Kaduna

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Kaduna, ta umarci a fara gudanar da cikakken bincike kan wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, wanda yake zargin jami’an ‘yan sanda suna tilasta wa masu motoci da babura ba su na goro yayin aiki a shingen bincike.

Kwamishinan rundunar, Rabi’u Muhammad ne ya bayar da umarnin inda ya buƙaci a gano su waye ne daga cikin ‘yan sandan aka gani a bidiyon kuma a gayyato su yayin binciken.

A wata sanarwa da Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan ya fitar a ranar Talata, rundunar ta ce dukkan jami’in da aka samu da hannu a laifin, zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada.

Haka kuma, hukumar ta bayyana cewa an riga da an soke tsarin bincike akan titina, saidai a wasu halaye da bincike ya nuna alamun zirga-zirgar masu aikata miyagun laifuka ko safarar haramtattun ababe.

A cewar sanarwar, wurin da aka nuna a bidiyon ya yi kama da wani sashe na yankin Millennium City, gurin da a kwanan nan ake alaƙantawa da miyagun ayyuka. A baya dai jami’ai sun gano wasu bindigogi ƙirar AK-47 guda 20 a wata hanya ta unguwar.

CP Muhammad ya ce, bai dace a ce sahihin ayyukan tsaro ya cakuɗa da matsa wa al’umma ba wajen tatsa ko cin fuskantarsu ba, yana mai jaddada haramcin amfani da kaki wajen cutarwa a madadin bayar da kariya.

By Babaji

Leave a Reply