
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Talata Gwamna Ademola Adeleke ya gabatar wa Shugaba Bola Tinubu shaidar lashe zaɓe bayan nasara da ya samu a zaɓen gwamnan Jihar Osun da aka gudanar a ranar 15 ga Agusta.
Adeleke tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar Accord Party ne suka kai wa Tinubu ziyara a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja da misalin ƙarfe 5:25 na yamma domin nuna godiyarsu ga shugaban kan yadda aka gudanar da zaɓen bisa tsarin doka.
Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa, Dada Olusegun, ya ce Adeleke ne ya jagoranci tawagar domin yaba wa shugaban ƙasar kan sakamakon zaɓen Osun.
A wani rubutu da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai na zamani, Olalekan Badmus, ya wallafa, an ga wani hoto da ke nuna yadda gwamnan ke gaisawa da Tinubu a fadar.

A ranar Laraba Adeleke ya karɓi takardar shaidar a ofishin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da ke Osogbo, kuma ya sanar da shirin samar da Naira miliyan 500 ga asusun waɗanda rikicin zaɓe ya shafa domin tallafa musu.
Adeleke dai ya lashe zaɓen na Osun ne bayan samun ƙuri’a 511,067, yayin da Oyebamiji ya samu 444,815. Najeem Salaam na ADC kuma ya samu 17,180, wanda aka gudanar a faɗin ƙananan hukumomi 30 na jihar

