Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da samar da fasfo a cibiyoyin Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) da dama, inda ta koma tsarin samar da fasfo a cibiya guda ta zamani.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin da yake duba sabuwar Cibiyar Samar da Fasfo ta Tsakiya (Centralised Passport Personalisation Centre) da ke hedikwatar NIS a Abuja.
Ministan ya ce tun bayan kafa Hukumar NIS a shekarar 1963, Nijeriya ba ta taɓa samun cibiyar samar da fasfo guda ɗaya da ke kula da samar da fasfo ga ƙasar baki ɗaya ba, har zuwa yanzu da aka aiwatar da wannan gagarumin sauyi.
Ya ce sabuwar cibiyar ta kammala aiki dari bisa ɗari, kuma za ta taimaka wajen ƙara sauri da ingancin ayyukan samar da fasfo ga ’yan Nijeriya.
Tunji-Ojo ya bayyana cewa tsofaffin injinan da ake amfani da su a baya suna iya samar da fasfo tsakanin 250 zuwa 300 ne kawai a kowace rana, yayin da sabuwar cibiyar ke da ƙarfin samar da fasfo tsakanin 4,500 zuwa 5,000 a kullum.
Ya ce hakan zai bai wa NIS damar biyan buƙatar fasfo ta yau da kullum cikin sa’o’i huɗu zuwa biyar kacal na aiki.
Ministan ya bayyana sabon tsarin a matsayin babban sauyi da zai kawo ƙarshen matsalolin jinkirin samar da fasfo da kuma inganta ayyukan hukumar.
Ya ce gwamnatin ta yi alkawarin samar da fasfo cikin makonni biyu, amma yanzu tana ƙoƙarin rage lokacin zuwa mako guda.
A cewarsa, amfani da na’urorin zamani da kuma inganta tsarin aiki su ne muhimman hanyoyin da za su taimaka wajen cika wannan alkawari ga ’yan Nijeriya.
Tunji-Ojo ya ce tsarin samar da fasfo daga cibiya guda ya yi daidai da ƙa’idojin da ake amfani da su a duniya, kuma zai taimaka wajen tabbatar da daidaito da kuma ƙara ingancin takardun tafiye-tafiyen Nijeriya a duniya.
Ya bayyana wannan sauyi a matsayin wani mataki na kusantar da ayyukan gwamnati ga ’yan Nijeriya, tare da samar da al’adar aiki cikin sauri, inganci da gaskiya a tsarin samar da fasfo.
Ministan ya ce tsarin ya yi daidai da ajandar sauye-sauyen Shugaba Bola Ahmed Tinubu, domin ƙara ƙarfin Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya da kuma inganta yadda ake samar da ayyuka ga jama’a.
