Daga MUHAMMADU MUJITAB a Kano
Shugaban Kwamitin Ilimi na Majalisar Dokokin Kano, Hon. Sulaiman Mukhtar Madobi, mai wakiltar ƙaramar Hukumar Madobi a Jihar Kano, kuma shugaban kwamitin gyaran dokokin ilimi na Kano, ya ce sama da shekaru 60 ana amfani da tsohon tsarin ilimi a Kano, tun daga zamanin Turawa.
Ya bayyana cewa bisa kishin Gwamna Abba Kabir Yusuf, Majalisar Dokokin Kano ta haɗa kai da gwamnan, inda a yanzu majalisar ta gyara dokokin ilimi na Kano domin su dace da ilimi, al’adu da addinin mutanen Kano.
Ya ce ana ƙoƙarin sanya hannu kan sabuwar dokar domin ta fara aiki, tare da bunƙasa ilimi a Kano.
Hon. Madobi ya bayyana hakan ne a lokacin rufe taron Daura Karatun Alƙur’ani Mai Girma, wanda hukumomin ƙasar Saudiyya suka ɗauki nauyin gudanarwa tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Kano. ɗan majalisar, Mukhtar, ne ya wakilci Gwamnan Kano a wajen taron.
Haka kuma, ɗan majalisar ya yaba wa dukkan masu ruwa da tsaki bisa nasarar shirya Daura Karatun Alƙur’ani Mai Girma.
Tun da farko, a jawabinsa, shugaban shirya taron Daura, Dakta Abdullahi Abdullahi Basulɓe, ya ce taron ya samu babbar nasara, domin jihohi 23 ne suka samu damar shiga gasar karatun.
Ya bayyana cewa haɗin gwiwar Gwamnatin Kano da hukumomin Saudiyya ya taimaka wajen gudanar da taron da ya samu nasara. Ya kuma yaba wa Jami’ar Khalifa Sheikh Rabi’u da sauran waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen nasarar taron.
