Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Yayin da miliyoyin masu amfani da wutar lantarki a Nijeriya ke ci gaba da fuskantar matsalar biyan kuɗin wutar da ba a auna yawan amfani da ita kai tsaye ba, sabon rahoto ya nuna cewa ana samun ci gaba wajen rage yawan masu amfani da wutar da ba su da mitoci. Sai dai har yanzu sama da kashi ɗaya bisa uku na masu amfani da wutar lantarki da ke aiki a ƙasar ba su da mitoci.
Sabbin alƙaluman Hukumar Kula da Harkokin Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) sun nuna cewa adadin masu amfani da wutar da aka sanya wa mitoci ya kai kashi 63.10 cikin 100 a watan Agustan 2026, daga kashi 62.37 cikin 100 a watan Yuli.
Wannan ci gaba ya kai adadin masu amfani da wutar da ke da mitoci zuwa 8,045,565, cikin jimillar masu amfani da wutar lantarki 12,749,789 a faɗin ƙasar. Hakan ya bar mutane 4,704,224 ba tare da mitocin auna yawan wutar da suke amfani da ita ba.
Alƙaluman sun nuna ana samun ci gaba a hankali, duk da cewa ba cikin sauri sosai ba. Adadin masu amfani da wutar da aka sanya wa mitoci ya ƙaru da kashi 1.8 cikin 100, daga 7,903,819 a watan Yuli. A lokaci guda kuma, yawan waɗanda ba su da mitoci ya ragu da mutum 63,752.
Sai dai saurin sanya sabbin mitocin ya ragu. Kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) sun sanya wa masu amfani da wuta 141,746 mitoci a watan Agusta, sabanin 159,980 da aka sanya a watan Yuli. Wannan ya nuna raguwar mitoci 18,234, kwatankwacin kashi 11.4 cikin 100.
Rahoton ya kuma nuna babban bambanci tsakanin kamfanonin rarraba wutar lantarki 11 na ƙasar wajen sanya mitoci ga masu amfani da wuta. Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Eko ne ya fi samun nasara, inda kashi 89.6 cikin 100 na masu amfani da wutarsa ke da mitoci. Kamfanin Ikeja Electric ya biyo baya da kashi 87.7 cikin 100, yayin da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja ya samu kashi 82.6 cikin 100.
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Fatakwal ya samu kashi 71 cikin 100, yayin da na Benin da Ibadan suka samu kashi 64.4 da kashi 59.2 cikin 100 bi da bi. Sai dai kamfanonin da ke Arewacin Nijeriya na ci gaba da yin baya wajen sanya mitoci. Kamfanin Jos ne ya fi kowa ƙarancin kaso, inda kashi 37.6 cikin 100 na masu amfani da wutarsa kaɗai ke da mitoci. Yola ya samu kashi 39.2 cikin 100, Kaduna kashi 42.3, yayin da Kano ya samu kashi 42.8 cikin 100.
Wannan na nuni da cewa masu amfani da wutar lantarki a yankunan da waɗannan kamfanoni ke kula da su na cikin haɗarin karɓar ƙididdigar kuɗin wuta ba tare da auna ainihin yawan wutar da suka yi amfani da ita ba, lamarin da kan haifar da saɓani tsakanin masu amfani da wutar da kamfanonin rarraba ta.
Sanya mitocin wutar lantarki na daga cikin muhimman hanyoyin tabbatar da gaskiya da adalci a harkar samar da wuta a Nijeriya. Idan babu mitoci, kamfanonin rarraba wutar kan ƙiyasta kuɗin da masu amfani za su biya maimakon auna ainihin yawan wutar da suka yi amfani da ita.
Wannan tsari ya jawo koke-koken masu amfani da hasken lantarki, asarar kuɗaɗen shiga ga kamfanoni da kuma raguwar amincewa tsakanin masu amfani da wuta da masu samar musu da ita.
