Mutum bakwai sun rasu yayin da 11 suka jikkata bayan tirela ta murƙushe motoci da babura a Gombe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wani mummunan hatsarin mota a yankin madakatar ababen hawa ta Magariya da ke garin Kumo a Ƙaramar Hukumar Akkon Jihar Gombe ya yi ajalin mutane bakwai tare da raunata wasu guda 11.

A cewar wata sanarwa da Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta fitar, hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin ranar Alhamis a yankin babban titin Gombe zuwa Ɓilliri. Bincike ya nuna cewa, an samu tsinkewar birki ne na wata tirela ƙirar DAF da ta nufi zuwa Yola a Jihar Adamawa daga Gombe, lamarin da ya yi sanadiyyar motar ta ƙwace daga hannun direbanta ta haye kan wasu ƙananan motoci biyu da babura biyar.

Mutanen 25 ne al’amarin ya shafa, yayin da FRSC ta tabbatar da cewa mutane bakwai sun rasu a nan take, waɗanda suka haɗa da manyan maza huɗu, ƙananan yara maza biyu da kuma wata yarinya. Sannan daga cikin mutane 18 da suka rayu, 11 sun samu raunuka kama daga ƙujewa mai tsanani, yanka mai zurfi da gocewar ƙashi da makamantansu. Sauran bakwai kuma sun tsira ba tare da sun samu wani rauni ba kuma tuni aka sallame su tun a wajen da abin ya faru.

Bayan samun kiran gaggawa da misalin ƙarfe 5:32 na yammacin ranar FRSC reshen Gombe ta tura jami’anta cikin mintina biyu domin bayar da agajin gaggawa. A yayin haka ne aka gaggauta kai waɗanda iftila’in ya shafa zuwa Babban Asibitin Tarayya da ke Kumo, inda aka hanzarta bayar da kulawar magani ga waɗanda suka jikkatan.

Wannan al’amari ya sake jefa al’umma cikin fargaba musamman kan yadda ake samun aukuwar irinsa a manyan titinan sassan Nijeriya, inda masu ruwa da tsaki suke maimaita kira ka a riƙa duba halin ire-iren motocin gabanin fara zirga-zirga akai-akai ta yadda za a samu sauƙin halayen jefa rayukan al’umma cikin haɗari.

By Babaji

Leave a Reply