Ƙungiyoyin ƙwadago sun yi barazanar shiga yajin aiki bayan tattaunawa da Gwamnatin Tarayya ta rushe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyoyin ƙwadago da suka haɗa da Nigeria Labour Congress (NLC) da Trade Union Congress (TUC) sun yi gargaɗin yiwuwar shiga yajin aikin gama-gari a faɗin Nijeriya bayan rashin cimma matsaya a tattaunawar da ya gudana tsakanin wakilanta da na Gwamnatin Tarayya kan buƙatun ma’aikata.

Ƙungiyoyin sun ce, za a ɗauki matakai na gaba ne bisa la’akari da sakamakon zaman da za a sake yi tsakanin ɓangarorin biyu, wanda za a gudanar a ranar 27 ga Oktoba, inda suka ƙara da cewa sun umarci rassansu na jihohi da su kasance a shirye domin tsunduma a yajin aiki muddin gwamnatin ta gaza ɗaukar matakan da suka dace kan al’amarin.

An bayyana haka ne a wani zama da aka gudanar a ranar Alhamis a ofishin Ma’aikatar Ƙwadago ta Tarayya da ke Abuja, wanda ke da nufin gabatar da buƙatun rage farashin fetur zuwa matakinsa na shekarar 2024, sake tattaunawa kan batun mafi ƙarancin albshi, aiwatar da matakan sauƙin haraji da cimma matsaya kan batun bashin albashin ma’aikatan lafiya da wasu ma’aikatan gwamnati.

A sanarwar haɗaka da NLC da TUC suka fitar ta hannayen manyan sakatarorinsu, Benson Upah da Nuhu Toro, ƙungiyoyin sun ce wakilan gwamnati ba su da ƙarfin gudanar da gamsashshen tattaunawa akan matsalolin don haka suka bayyana rashin gamsuwa da sakamakon zaman.

A cewar sanarwar, an ɗage zaman ne zuwa ranar 27 ga Oktoban domin bai wa gwamnatin damar kimtsawa da tabbatar da dukkan wakilan cibiyoyinta masu ruwa da tsaki sun samu halarta. Sun bayyana cewa, a shirye suke su karɓi tattaunawa amma ba za su lamunci jinkirin tsawon lokaci ba.

By Babaji

Leave a Reply