Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta dawo da tsarin tallafin man fetur ba, yana mai cewa gwamnatinsa ta ɗauki mataki mai ƙarfin hali kuma wajibi ne domin yin gyare-gyare ga tattalin arzikin ƙasar.
Jaridar News Point Nigeria ta ruwaito cewa Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, yayin wani taro da ƙungiyar City Boy Moɓement, wadda matasa suka kafa domin yaɗa manufofin gwamnatinsa da kuma tallafa mata.
“Ina zuwa, a rana ta farko na cire tallafin mai. Da ba haka ba, Nijeriya za ta yi fatara; babu abin da ya rage da za a biya tallafin mai da shi,” inji shi.
Ya ƙara da cewa: “Zan iya sauraron abokan hamayyata na siyasa suna alƙawarin dawo da tallafin mai.”
Da yake amfani da misali daga addini, shugaban ƙasar ya ce: “Ina tuna karatuna na nassosin addini, na Littafi Mai Tsarki da kuma Alƙur’ani mai girma. Lokacin da Annabi Musa (Musa) ya bar Masar, Tekun Maliya ya rabu, ya ba shi hanya. Ba za ka iya cewa Musa ya koma Masar ba. Da ƙarfin ku da goyon bayanku, ba za mu taɓa komawa Masar ba.”
Tsohon gwamnan Jihar Legas ya yaba wa ƙungiyar bisa ƙoƙarin da take yi na neman goyon baya ga gwamnatinsa, sannan ya buƙaci mambobinta su kai saƙon nasarorin gwamnatinsa zuwa matakin talakawa.
“Ku waɗanda kuka yi sa’ar yin aiki tare da ni, kun ba ni dukkan amsoshin da ake buƙata da kuma kwarin gwiwar kallon zaɓe mai zuwa a matsayin abu mai sauƙi,” inji Tinubu.
Ya ci gaba da cewa: “Za ku je makarantunku na gaba da sakandare, kasuwanninku da ƙauyukanku. Ku tabbatar cewa duk matashin da kuka sani yana da katin zaɓe na PɓC kuma yana amfani da shi. Ku gaya musu abin da muka yi da abin da za mu yi. Ku gudanar da kamfen da dabarunku da ra’ayoyinku.”
Shugaba Tinubu ya sanar da kawo ƙarshen tallafin man fetur ne a lokacin rantsar da shi a watan Mayun 2023. Matakin ya haifar da tashin farashin man fetur nan take, inda farashin lita ya tashi daga ƙasa da naira 200 zuwa tsakanin naira 1,350 da naira 1,405 a manyan gidajen mai.
Duk da cewa matakin ya jawo suka daga ɓangarori da dama saboda yadda ya ƙara tsadar rayuwa, shugaban ƙasar ya ci gaba da tsayawa kan matsayinsa na ƙin dawo da tallafin man fetur.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa matakin yana da muhimmanci wajen sake fasalin tattalin arzikin ƙasa, tare da tabbatar wa ’yan ƙasa cewa matsin tattalin arzikin da aka fara fuskanta zai ragu a hankali yayin da lokaci ke tafiya.
