Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Al’ummar Marghi mazauna Jihar Kano sun gudanar da gagarumin bikin al’ada na Yawal, tare da bikin murnar cika shekara ɗaya da naɗin Wadzani Adamu Mamza a matsayin Ptil Marghi na Kano.
Taron, wanda ya gudana ranar Asabar a Kano, ya haɗa da naɗin sababbin Bulama da Lawan, waɗanda za su zama wakilan sarki a unguwanni. Taron ya samu halartar sarakuna, jami’an gwamnati, ’yan siyasa, shugabannin ƙabilu da ɗaruruwan ’yan Marghi.
Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Hon. Umar Haruna Doguwa, wanda ya halarci taron tare da tawagarsa, ya bayar da gudummawar naira miliyan ɗaya (N1m).
Hon. Doguwa ya bayyana al’ummar Marghi a matsayin masu son zaman lafiya da ci gaban al’umma.
Ya ce Jihar Kano, a ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, tana zaune da ƙabilu daban-daban cikin zaman lafiya.
“Rayar da al’ada na da amfani. Duk inda kake, riƙe al’adarka zai riƙe maka mutuncinka,” in ji shi.
Da yake jawabi, Mai Martaba Ptil Marghi na Kano, Wadzani Adamu Mamza, ya gode wa Allah da al’ummar Marghi bisa amincewar da suka nuna masa.
Ya bayyana ranar a matsayin ranar farin ciki guda uku: bikin Yawal, cika shekara ɗaya a kan karaga da kuma faɗaɗa majalisar gargajiya ta Marghi a Kano.
Game da al’ada, sarkin ya yi kira ga iyaye da su riƙa magana da ’ya’yansu da harshen Marghi. Ya kuma ja hankalin matasa da su riƙa alfahari da sanya kayan Marghi da kuma yin rawar gargajiya.
“Domin idan muka rasa al’adunmu, mun rasa kanmu,” in ji shi.
Ya ce a shekarar da ta gabata, ya yi alƙawarin haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba, kuma Allah ya taimaka aka cimma hakan tare da haɗin kan dattawa, mata da matasa.
Da yake sanar da naɗin sababbin Bulama da Lawan na Ptil Marghi na Kano, ya ce mukaman da aka ba su ba na alfahari ba ne, domin hidima ce ga al’umma.
Ya ja hankalinsu da cewa: “Ku jagoranci mutanenku da tsoron Allah, adalci, tawali’u da gaskiya. Fadarku ta zama fadar zaman lafiya ga kowa. Kada ku yi amfani da mukaminku wajen zalunci ko aikata wani abu da ya saɓa wa ƙa’ida,” inji shi.
Tun da farko, a jawabinsa, Sakataren Ptil Marghi na Kano, Mista Zakariya Yusuf Midala Uɓu, ya bayyana bikin a matsayin mai tarihi.
Ya yi nuni da cewa: “Yawal godiya ce ga Allah bisa albarkar girbin amfanin gona da aka samu, da kuma yin addu’ar neman zaman lafiya. Haka kuma, makaranta ce inda ’ya’yanmu ke koyon jarumtaka, aiki tuƙuru da gaskiya.
“Ta wannan biki a Kano, duk da nisan da ke tsakaninsu da tsaunukansu, suna bayyana cewa al’adunsu ba za su taɓa mutuwa ba, kuma harshensu ba zai taɓa ɓacewa ba,” in ji shi.
Ya ce a cikin shekara ɗaya, Mai Martaba Ptil Marghi na Kano ya haɗa dukkan ƙungiyoyin Marghi ƙarƙashin lema ɗaya. Ya kuma gina kyakkyawar alaƙa da Masarautar Kano da Gwamnatin Jihar Kano, tare da farfaɗo da ƙungiyar rawa ta al’ada da kuma ajin koyon harshen Marghi ga yaran da aka haifa a Kano.
Da yake bayar da tarihin al’ummar, Shugaban ƙungiyar Raya Al’ummar Marghi ta Kano, Elder Apagu Awanuwai Wabba, ya ce zuwan Margawa Kano ya fara ne tun a shekarun 1940 domin kasuwanci.
Ya ce an kafa ƙungiyar al’ummar a shekarar 1962 a Unguwar Brigade, wadda daga baya ta rarrabu zuwa rassa saboda yawaitar jama’a.
Ya ce a yau, al’ummar Marghi suna da yawa a Panshekara, Sharada, Bompai, Farawa, Tudun Murtala, Badawa, Rimin Kebe da Darmanawa.
Elder Wabba ya ce an zaɓi Wadzani Adamu Mamza a farkon shekarar 2025, sannan aka naɗa shi sarauta a ranar 18 ga Oktoba, 2025.
“A cikin shekara ɗaya, Mai Martaba Wadzani Adamu ya tabbatar da cewa ɗan albarka ne. Ya haɗa kan al’ummar Marghi, kuma ya dawo da mutunta al’ada da zaman lafiya,” in ji Wabba.
A yayin taron, an gudanar da raye-rayen gargajiya, nuna kayan al’adar Marghi da addu’o’in neman tsawon rai ga Mai Martaba, da kuma zaman lafiya a Jihar Kano da Nijeriya baki ɗaya.
