Sarkin Rano ya naɗa sabbin dagatai uku a masarautar

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Mai Martaba Sarkin Rano, Alhaji Muhammad Isah Umar, ya naɗa sabbin dagatai uku a masarautarsa a ranar Litinin da ta gabata.

Sarkin ya ce masarautar ta yi nazari mai zurfi kafin ta naɗa su a waɗannan muƙamai, bisa la’akari da yadda suke gudanar da hulɗarsu da jama’a.

Ya ja hankalinsu da su zauna lafiya da al’ummomin da suke jagoranta.

Ya kuma yi kira gare su da su haɗa kai da malamai, limamai, matasa, jami’an lafiya da jami’an tsaro domin ci gaban yankunansu.

Sarkin ya ba su shawarar kula da tarbiyyar yara da kuma tabbatar da cewa suna zuwa makarantun boko da na addini.

Haka kuma, ya gargaɗe su da su guji aikata duk wani abu da zai cutar da al’ummomin da suke shugabanta, ko haɗa kai da wasu wajen zaluntar al’ummar.

Ya yi musu fatan alheri da samun nasara, tare da umartarsu da su ci gaba da gudanar da addu’o’i domin samun zaman lafiya a ƙasar nan.

Su ma a nasu ɓangaren, sabbin dagatan sun nuna farin cikinsu tare da gode wa sarkin bisa zaɓen da ya yi musu da naɗa su a waɗannan muƙamai.

Sun tabbatar da cewa za su yi amfani da shawarwarin da ya ba su domin kawo ci gaba a yankunansu.

Sun kuma bayyana gamsuwarsu da shawarwarin da sarkin ya ba su, tare da cewa za su haɗa kai da duk wata hukuma ko ƙungiya da ta zo yankunansu domin aiwatar da ayyukan ci gaba a garuruwansu.

Waɗanda aka naɗa sun haɗa da Alhaji Umar Ibrahim, a matsayin Dagacin Barkun; Alhaji Ali Danbaba, a matsayin Dagacin Tugugu; da Alhaji Nasiru Abubakar, a matsayin Dagacin Lautaye.

By ukarofi

Leave a Reply