
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta jaddada aniyar shirinta na tura jami’ai a faɗin Nijeriya domin sanya ido akan lamuran tauye mudu a kasuwanni, gidajen mai, manyan shagunan siyayya da wasu cibiyoyin kasuwanci.
Daraktan reshen kula da harkokin awon sikeli (WMD) na Ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci da Zubar, Dakta Salim Mohammed ne ya bayyana haka a wata hira da ‘yan jarida a Abuja. Ya ce, reshen nasu zai haɗa gwiwa da Hukumar kula da Lamuran Gasa da Bai wa Kwastomomi Kariya (FCCPC) da Cibiyar Kula da Yanayin Sharuɗɗan Gudanarwa ta Ƙasa (NMI-SON) domin aiwatar da shirin.
“Kada a cutar da mai saye, kuma kada a cutar da mai siyarwa. Awo na daidai shi ne ginshin samar da yardar da aminci a kasuwanci,” inji shi. Ya bayyana cewa, an yi wa shirin take ne da: ‘Full Measure, Fair Trade,” wanda ya zo a daidai lokacin da al’umma suke fuskantar matsin halin tattalin arziƙi a ƙasar. “A halin matsin tattalin arziƙi, kowace lita da aka tauye da kowane awon kilogram da aka yi ha’inci a kai, ƙarin matsi ne akan talakawa magidanta,” inji daktan.
A cewarsa, shirin, wanda za a ƙaddamar nan ba da jimawa ba, ya ƙunshi sanar da ayyukan tantancewa, zuwa ziyarar ba-zata a wuraren da aka tsara nazari akansu, siyan wasu kayayyaki don gwaji da kuma ayyukan tilasta biyayya ga dokoki, yana mai ƙarawa da cewa, za a fitar wa al’umma sakamakon bincike da kuma sunayen waɗanda aka kama da laifi. Kazalika ya ce, za a yi amfani sa maunan da aka amince da su ne a dokance.
