Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Hukumar tsaro ta civil defence ta Najeriya (NSCDC), Kwamandan Jihar Zamfara, ta kama wani direban haya ɗan shekara 24 bisa zargin hannu a harkar safarar miyagun ƙwayoyi masu ƙarfi ba bisa ƙa’ida ba.
Hukumar ta ce wanda ake zargin, Abdulraheed Abdullahi, ɗan asalin ƙauyen Bagega ne da ke ƙaramar hukumar Anka, an kama shi a ranar 18 ga Oktoba, 2026, a wani shingen bincike da ke ƙaramar hukumar Anka a lokacin da yake riƙe da sinadaran da ake zargin ƙwayoyi ne masu ƙarfi.
A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis kuma shugaban hulɗa da Jama’a, ASCI Umar Mohammad M. ya sanya wa hannu, hukumar ta ce kama shi ya yi daidai da aikin da doka ta ba ta da kuma haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro.
A cewar sanarwar, an miƙa shari’ar daga ofishin NSCDC na ƙaramar hukumar Anka zuwa hedikwatar Jihar da ke Gusau a wannan rana.
Hukumar ta bayyana cewa an ɓoye sinadaran da aka haramta aka kuma ƙunsa su a cikin kwalbar taliyar Indomie.
Wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa ya karbi ƙunshin ne daga wani memba na ƙungiya wanda a halin yanzu yake a guje.
Kayan da aka ƙwato a cewar hukumar sun haɗa da sachets 50 na Lara Tramadol, fata 2 dauke da Methamphetamine (ice), guda 1000 na ƙwayoyin Diazepam (D5), da kuma dami na wiwi guda biyu.
Hukumar ta bayyana cewa tuni ta bayar da umarnin miƙa shari’ar nan take zuwa hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakin da ya dace.
NSCDC ta jaddada cewa ba ta lamuntar aikata laifuka, tana mai jaddada cewa ƙarƙashin jagorancin kwamanda janar, Farfesa Ahmed Abubakar Audi, mni OFR, da kwamandan Jihar, CC Sani Mustapha, hukumar ta himmatu wajen tabbatar da adalci ga farar hula tare da ɗaukar matakai masu inganci na hana da kuma kawar da ayyukan da ba bisa ƙa’ida ba.
