An buƙaci gwamnatin Katsina ta ƙirƙiro dandali na malaman jami’o’i da manyan makarantu

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban kwamitin shirya makon ɗaliban Jihar Katsina, kuma mai ba gwamnan Jihar Katsina shawara kan ayyukan ƙananan hukumomi, Hon. Lawal Rufa’i Safana, ya jagoranci kwamitin wajen gudanar da bikin rufe makon ɗaliban Jihar Katsina na farko na shekarar 2026, wanda aka gudanar a Jami’ar Umaru Musa Yar’Adua (UMYU), Katsina.

Taron, wanda ya samu halartar Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya zama wani muhimmin mataki na ƙarfafa alaƙa tsakanin ɗalibai da gwamnati, tare da samar da damar tattaunawa kan ci gaban ilimi, walwalar ɗalibai da bunƙasa ƙwarewar matasa. Ɗalibai daga manyan makarantu 55 ne suka halarci shirin, wanda aka gudanar ƙarƙashin ofishin mataimaki na musamman ga gwamna kan harkokin ɗalibai, Hon. Muhammad Nuhu Nagaske.

A jawabinsa a wajen taron, Hon. Lawal Rufa’i Safana ya buƙaci Gwamnatin Jihar Katsina da ta samar da wani dandali na musamman da zai haɗa malaman jami’o’i da sauran manyan makarantu daga sassa daban-daban na Najeriya, domin tattaunawa da musayar ra’ayoyi kan batutuwan da suka shafi ci gaban jihar da inganta shugabanci.

Safana ya bayyana cewa, irin wannan dandali zai samar da damar da gwamnati za ta riƙa tattaunawa da malamai, tare da neman shawarwarinsu da gudummawarsu wajen samar da mafita ga ƙalubalen da ke addabar jihar. Ya ƙara da cewa, bisa lura da ya yi a matsayinsa na shugaban kwamitin shirya shirin, kafa wannan dandali zai taimaka wajen ƙarfafa haɗin kai, zumunci, tattaunawa da gudanar da bincike kan muhimman batutuwan ci gaba.

A cewarsa, haɗa ƙwararrun malamai da masu bincike a wuri guda zai ba su damar bayar da shawarwari masu amfani da za su taimaka wajen tsara manufofi da inganta ayyukan gwamnati, tare da samar da gudummawar da za ta amfani jihar Katsina a nan gaba.

Ya kuma jaddada muhimmancin ci gaba da gudanar da makon ɗaliban Jihar Katsina a kowacce shekara, domin ƙarfafa dangantaka tsakanin ɗalibai da gwamnati, samar da damar tattaunawa kan ƙalubalen karatu da walwala, da kuma bai wa matasa damar taka rawa wajen ci gaban jihar.

A nasa jawabin, Gwamna Raɗɗa ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da tallafa wa ɗalibai, waɗanda suka kammala karatu da matasa masu fasahar ƙirƙire-ƙirƙire, ta hanyar faɗaɗa damar samun ilimi, horar da sana’o’i da bunƙasa harkokin kasuwanci. Ya kuma buƙaci malaman jami’o’i, farfesoshi da masu bincike ’yan asalin jihar Katsina da su kafa ƙungiya da za ta taimaka wa gwamnati da shawarwari da bincike wajen magance ƙalubalen da ke fuskantar jihar.

A nasa ɓangaren, mataimaki na musamman ga gwamna kan harkokin ɗalibai, Hon. Muhammad Nuhu Nagaske, ya yaba wa Gwamna Raɗɗa bisa goyon bayan da yake bai wa ɗalibai da matasa masu fasahar ƙirƙire-ƙirƙire, musamman amincewa da tallafin ₦500,000 ga masu ƙirƙire-ƙirƙire da suka halarci wani taro a cibiyar Kano.

Bikin rufe nakon ɗaliban Jihar Katsina na farko ya ƙara nuna muhimmancin haɗin guiwa tsakanin gwamnati, ɗalibai da ƙwararrun malamai wajen samar da mafita ga ƙalubalen ilimi, bunƙasa bincike da ƙwarewa, da kuma shirya matasa domin taka muhimmiyar rawa a ci gaban jihar Katsina.

By ukarofi

Leave a Reply