2027: INEC ta gargaɗi ‘yan siyasa da jami’ai kan maguɗin zaɓe, ta yi barazanar hukuncin zaman kurkuku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, ta fitar da gargaɗi ga ‘yan siyasa, wakilan jam’iyyu da jami’anta akan ayyukan maguɗin zaɓe a yayin gudanar da zaɓukan 2027, tana mai cewa hakan ka iya sa a tasa ƙeyar dukkan wanda aka samu da hannu a ciki zuwa gidan yari da cin sa tara.

Kwamishinan zaɓe na shiyya (REC) a Jihar Filato, Farfesa Samuel Egwu ne ya bayar gargaɗin a Jos, ranar Talata, 20 ga Oktoba, 2026, yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki, jagororin jam’iyyun siyasa da ‘yan takara gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Egwu ya bayyana zaman a matsayin muhimmin al’amari gabanin gudanar da zaɓukan, yana mai cewa jam’iyyun siyasa da ‘yan takara suna da gagarumar rawar takawa wajen tabbatar da sahihancin zaɓe. A cewarsa, sun kira zaman ne da nufin sanar da masu ruwa da tsaki muhimman al’amuran zaɓe tare da tunatar da su nauye-nauyen doka da suka rataya akansu.

Ya bayyana cewa, laifukan zaɓe musamman waɗanda suka shafi sahihancin ƙuri’u, ka iya janyo ɗaukar matakan shari’a akan mutum, ciki har da zuwa kurkuku da biyan tara muddin aka samu mutum da hannu a ciki.

Baturen zaɓen ya kuma yi gargaɗi akan yawaitar kashe kuɗi yayin zaɓuka, duk da cewa yaƙin neman zaɓe na buƙatar kashe kuɗi, amma hakan ba shi ke bayar da damar almubazzaranci da kuɗaɗe ba, wanda yin hakan ka iya haifar da tsaiko ga sahihancin zaɓe. “Kuɗi na da matuƙar muhimmanci a lamuran zaɓe. Kai, idan ma aka ce babu kuɗi, ba za ka iya fitowa takara ba. Amma idan ka raba kuɗaɗe masu yawa, hakan kuma zai iya zama matsala,” inji shi.

Da yake jawabi a taron, Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Filato, Faniyan Ayodeji, wanda ya samu wakilcin Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda na sashen Atisaye, Nengi Jephtha, ya ce biyayya ga bayanai da sharuɗɗan zaɓe suna da muhimmanci wajen bayar da kariya ga rikici ko tarzoma yayin zaɓuka, yana mai tabbatar da cewa rundunar ta duƙufa wajen ganin an gudanar da sahihan zaɓuka cikin aminci bisa samun haɗin kan ‘yan siyasa wajen kiyaye dokokin zaɓe.

By Babaji

Leave a Reply