
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Shugaban Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), Sheikh Abdullahi Usman Saleh Pakistan, ya yi gargaɗin cewa rashin bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu damar sake mulkar Nijeriya a babban zaɓen 2027 ka iya haifar da rikicin siyasa a ƙasar.
Sheikh Pakistan ya bayyana haka ne yayin jawabi ga wata ƙungiyar matasa a gidansa da ke Kano, inda ya ce akwai buƙatar a ƙyale Tinubu ya yi wa’adi na biyu domin kiyaye tsarin karɓa-karɓa tsakanin Kudu da Arewa, kamar yadda aka ƙyale marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi wa’adin mulki biyu.
Tsohon shugaban na NAHCON ya bayar da misali da bunƙasar lamuran tsaro a babban titin Abuja zuwa Kaduna da samun sauƙin hauhawar farashin kayayyaki a matsayin ribar da aka samu a ƙarƙashin gwamnatin jam’iyyar APC. A cewarsa, gwamnatin Tinubu ta gaji manyan ƙalubalen tsaro guda biyu: fitinar Boko Haram, wadda aka fara tun kafin hawan Buhari kujerar shugaban ƙasa, da kuma ayyukan ɓarayin daji da ‘yan bindiga da aka fara a zamanin Buhari.
“Idan kuka kalli matsalar tsaro wadda da ita wasu ‘yan siyasa suke kamfen, har zuwa lokacin da Buhari ya zama shugaban ƙasa, babu batun garkuwa da mutane. Babu garkuwa da mutane a jihohin Zamfara, Kaduna, Sakkwato da Kebbi”, inji Shehin malamin.
Ya kuma yi gargaɗin siyasar ƙabilanci ka iya haifar da koma-baya ga ƙasar, yana mai ƙalubalantar yaƙar sake zaɓar Tinubu saboda matsalar ɓangaranci, inda ya kuma ce ƙiyayyar jagororin siyasa saboda bambancin shiyya abu ne da zai iya haddasa gagarumar ƙalubale ga ƙasar a nan gaba. “Ya kamata mu yi wa Tinubu adalci. Irin siyasar da muke yi na ƙin mutum don saboda shiyyar da ya taho tana da matuƙar hatsari. Idan muka cigaba da tafiya a haka, za mu sha wahala nan gaba,” inji shi.
Kazalika, ya tunatar da lokacin da Tinubu ya bai wa marigayi Buhari goyon baya a lokacin da yake fama da rashin lafiya na cewa lallai ya dace ya kammala wa’adin mulkinsa na biyu duk da halin rashin lafiyar, yana mai cewa hana Tinubu yin wa’adi na biyu ka iya jefa ƙasar cikin rikicin siyasa.
Har ila yau, ya bayan halin tsaro a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a lokacin Buhari da kuma a zamanin mulkin Tinubu, inda ya ce tafiya a wancan lokaci a hanyar na da matuƙar hatsari saboda matsalar rashin tsaro, amma a yanzu ana tafiya cikin aminci ba tare da wata fargaba ba hatta a tsakiyar dare.
Ya ƙara da cewa, hatta a fannin farashin kayan abinci, an samu sauƙi a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu akan kafin hawansa mulki, yana mai bayar da misali da farashin shinkafa da gero. Ya ce, ana siyar da buhun shinkafa akan N120,000 a lokacin Buhari, amma yanzu a N57,500 ake siya, wato ƙasa da rabin farashin baya. Farfesan, wanda ya bayyana kansa a matsayin manomi, ya haɗa farashin gero a baya da yanzu zamanin Tinubu. Ya ce: “…a ƙarƙashin Buhari ina siyar da buhun gero akan N85,000. Amma a yau ana siyarwa akan kusan N30,000.”
