
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Cibiyar Kula da Bada Kariya ga Cututtuka ta Ƙasa NCDC, ta bayyana cewa matar da aka gano tana ɗauke da cutar Ebola ta shigo Nijeriya ne a ranar 5 ga Oktoba, wadda aka ga alamun cutar a tare da ita bayan kwanaki biyu sannan aka garzaya da ita wani asibitin kuɗi da ke Babban Birnin Tarayya (FCT) Abuja a ranar 11 ga Oktoba.
Manajan kula da lamuran cutar Ebola na Ƙasa, Dakta Odianosen Ehiakhamen ne ya bayyana haka a wata hira da gidan talabijin na Arise a ranar Talata. Ehiakhamen, wanda kuma mataimakin darakta ne a NCDC, ya bayyana cewa da fari an yi wa mara lafiyar magani ne akan cutar zazzaɓin cizon sauro bisa alamun da aka gani, kana daga bisani likitoci suka fara zargin tana ɗauke da Ebola gabanin ta bar ƙasar Uganda zuwa Nijeriya.
A ranar Talata ne dai Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da ɓullar cutar a karon farko a Abuja bayan an gano cewa wata mata da ta zo Nijeriya daga Uganda ɗauke da ita. Ministan Lafiya da Walwalar Al’umma, Farfesa Ali Pate, wanda ya sanar da labarin, ya ce an gano wasu mutane 44 da ke ɗauke da alamun cutar, waɗanda aka ware su kuma ake kula da su, ciki har da ma’aikatan lafiya, marasa lafiya, masu aikin raino da wasu mutanen da ake zargin sun shigo Nijeriya ne tare da matar.
Tuni dai aka ware mara lafiyar ake ba ta kulawar magani, yayin da hukumomin lafiya suke ƙoƙarin gano matakin ɓullar cutar tare da kare yaɗuwarta acikin al’umma. A cewar Ehiakhamen, asibitin da aka kwantar da matar ne ya sanar da NCDC halin da ake ciki a ranar Talatar bayan sun fahimci cewa matar ba ta samun sauƙi daga maganin da ake mata, lamarin da ya haifar da ɗaukar jini tare da gudanar da aikin gwaje-gwaje a kai. A yayin haka ne aka gano cewa matar tana ɗauke da cutar Ebola, wadda aka gabatar a ranar 11 ga Oktoba, inda tuni aka hanzarta sanar da sauran hukumomin lafiya tare da ɗaukar matakan da suka dace domin kare cigaba da yaɗuwarta.
Babban jami’in lafiyar ya kuma jinjina wa hukumomin lafiyar FCT bisa hoɓɓasa da suka yi a lokacin da ya dace, yana mai cewa tawagar ta samar da takardar rahoton bincike kuma ta samu bayanai daga aikin likitan da ya kula da al’amarin.
Ya ƙara da cewa, mafi yawancin mutane 44 da aka keɓancen ma’aikatan lafiya ne da ma’aikatan da suka taimaka a asibitin a lokacin da ake yi wa mara lafiyar magani. Kazalika, ya ce Nijeriya ta fara shirye-shirye akan yiwuwar ɓullar cutar Ebola tun tsawon watanni kafin a tabbatar da ɓullarta a ƙasar, bayan an samu rahotannin ɓarkewarta a wasu ƙasashe.
