Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya ƙaddamar da manufofin sauyin yanayi na Jihar Katsina, tare da ƙaddamar da littafin tarihin nasarorin da gwamnatinsa ta samu a fannin sauyin yanayi, mai taken Governor Dikko Raɗɗa Climate Legacy Publication.
Wannan mataki ya ƙara ƙarfafa aniyar gwamnatinsa na kare muhalli, bunƙasa makamashi mai sabuntawa da samar da ci gaba mai jure wa sauyin yanayi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen taron ƙoli karo na biyu kan ayyukan yaƙi da sauyin yanayi da zuba jari a fannin tattalin arziƙin kore na shekarar 2026, wanda aka gudanar a Abuja mai taken: “Ƙarfafa jagorancin Katsina a fannin sauyin yanayi: Ƙaddamar da manufofin sauyin yanayi na Jihar Katsina da littafin tarihin nasarorin Gwamna Dikko Raɗɗa.”
Raɗɗa ya bayyana sauyin yanayi a matsayin babban ƙalubalen ci gaba da ke shafar noma, albarkatun ruwa, lafiyar jama’a, ababen more rayuwa da hanyoyin samun abin dogaro da kai. Ya jaddada cewa dole ne kare muhalli ya kasance cikin manyan abubuwan da jihar ta sanya a gaba wajen gudanar da ayyukan ci gaba.
“Kare muhalli ba zai yiwu ba tare da kare rayuka da hanyoyin samun abin dogaro da kai ba, da ƙarfafa tattalin arziƙinmu da kuma tabbatar da kyakkyawar makoma ga yaranmu,” in ji Dikko.
Gwamnan ya bayyana cewa ƙaruwar zafi, sauye-sauyen yanayin ruwan sama, yaɗuwar hamada, lalacewar ƙasa da ambaliyar ruwa na buƙatar tsare-tsare masu haɗin kai, hukumomi masu inganci, hanyoyin samar da kuɗaɗen gudanarwa masu ɗorewa da kuma sa hannun al’umma wajen aiwatar da shirye-shirye.
Ya bayyana cewa yaƙi da sauyin yanayi dole ne ya samar da sakamako na zahiri, ciki har da inganta noma, samar da makamashi mai tsafta, farfaɗo da wuraren da muhalli ya lalace da kuma ƙarfafa juriyar al’umma ga matsalolin muhalli.
Dangane da shugabanci a fannin sauyin yanayi, Raɗɗa ya ce maki 3.0 da aka bayyana cewa jihar Katsina ta samu a ma’aunin tantance ayyukan shugabancin sauyin yanayi na jihohi na shekarar 2026, ya nuna ci gaban da aka samu wajen inganta tsarin kula da muhalli.
Sai dai ya jaddada cewa irin wannan karramawa dole ne ta haifar da sauye-sauye masu nunawa a rayuwar jama’a.
Gwamnan ya bayyana shirin Katsina One Tree Initiative, wato shirin dasa bishiya guda ɗaya ga kowane mutum, a matsayin wani babban shiri da aka ƙaddamar domin bunƙasa al’adar kula da muhalli tsakanin mazauna jihar, makarantu, hukumomi, ‘yan kasuwa da al’ummomi.
“Manufarmu ita ce mu tattara kusan mazauna Jihar Katsina miliyan 11 domin kowannensu ya dasa bishiya aƙalla guda ɗaya tare da kula da ita har zuwa shekarar 2030,” in ji shi.
Radda ya bayyana cewa shirin yana da burin dasa bishiyoyi miliyan biyu kafin ƙarshen shekarar 2026, yana mai jaddada cewa kula da bishiyoyin bayan dasa su da kuma sanya ido a kansu na da matuƙar muhimmanci domin tabbatar da cewa sun rayu.
“Wannan ba shirin dasa bishiyoyi kawai ba ne; ƙoƙari ne na gina al’adar kula da muhalli a faɗin jiharmu,” in ji shi.
A fannin makamashi mai sabuntawa, Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa an riga an samar da ƙarfin makamashi mai sabuntawa da ya haura megawatt 30, a matsayin wani ɓangare na cimma burin jihar na kaiwa megawatt 70 nan da shekarar 2031.
Ya kuma yi tsokaci kan shirin gwamnatinsa na samar da hasken fitilun tituna masu amfani da hasken rana, wanda rahotanni suka nuna cewa ya kai kusan kilomita 85, tare da kashe kuɗaɗen da suka haura naira biliyan 7.6.
Raɗɗa ya bayyana cewa zuba jari a makamashi mai sabuntawa zai inganta samar da wutar lantarki ga makarantu, cibiyoyin lafiya, harkokin noma, kasuwanci da masana’antu, tare da samar da damammaki ga harkokin kasuwancin kore da samar da ayyukan yi.
Ya ce jihar za ta ci gaba da nazarin hanyoyin zuba jari a samar da wutar lantarki ta hasken rana, ƙananan hanyoyin rarraba wutar lantarki, noma mai ɗorewa, sarrafa shara, gine-ginen da ke amfani da makamashi yadda ya kamata da sauran fannoni masu taimakawa wajen kare muhalli.
Gwamnan ya bayyana ƙaddamar da manufofin sauyin yanayi na Jihar Katsina a matsayin wani babban ci gaba wajen tsara yadda jihar za ta tunkari ƙalubalen muhalli.
Ya bayyana cewa manufofin za su zama jagora wajen shigar da batutuwan sauyin yanayi cikin tsare-tsaren ci gaba da kasafin kuɗi, ƙarfafa haɗin gwiwar hukumomi, samar da kuɗaɗen yaƙi da sauyin yanayi da kuma kafa hanyoyin auna ci gaban da aka samu.
“Ƙaddamar da waɗannan manufofi wani muhimmin mataki ne na ci gaba, amma ainihin nauyin da ke kanmu zai fara ne daga tabbatar da an aiwatar da su yadda ya kamata,” in ji shi.
Gwamnan ya yi kira ga ma’aikatu, sassa, hukumomi da ƙananan hukumomi da su shigar da batutuwan sauyin yanayi cikin shirye-shiryensu, su fayyace nauyin da ke kan kowane ɓangare tare da ƙarfafa sa ido domin tabbatar da cewa zuba jarin da ake yi yana samar da sakamako mai ma’ana ga muhalli da al’umma
Gwamnan ya kuma yi tsokaci kan gasar kyautar kore ta ɗalibai ta Gwamna Raɗɗa ta shekarar 2026, wadda aka ƙaddamar domin wayar da kan jama’a game da muhalli da kuma ƙarfafa matasa su samar da hanyoyin magance ƙalubalen sauyin yanayi.
Yayin da yake taya waɗanda suka lashe kyaututtukan murna, ya yaba da ƙirƙirarsu tare da amincewa da gudummawar malamansu, makarantu da iyalansu.
“Matasa za su gaji sakamakon matakan da muka ɗauka game da muhalli, hukumomin da muka gina da albarkatun ƙasa da muka kare—ko muka gaza karewa,” in ji shi.
Gwamnan ya yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya, abokan hulɗar ci gaba, cibiyoyin kuɗi, ƙungiyoyin bincike, ƙungiyoyin farar hula da kamfanoni masu zaman kansu domin faɗaɗa ayyukan yaƙi da sauyin yanayi a Jihar Katsina.
