Ba mu tabbatar da ɓullar cutar Ebola ba a ƙasarmu, inji hukumomin Uganda

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ma’aikatar Lafiya ta ƙasar Uganda ta ce ba ta tabbatar da wani rahoton ɓullar cutar Ebola ba a ƙasarta, inda ta ce matar da aka ce an samu da cutar a Abuja, ‘yar Nijeriya ce ta da yi tafiya daga wata ƙasa zuwa Nijeriya ta Uganda.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata mai ɗauke da sanya hannun Darakta-Janar ɗinta na Harkokin Lafiya, Charles Olaro, ma’aikatar ta ce matar ta je gabashin ƙasar Dimukraɗiyyar Jamhuriyar Kongo (DRC) ne domin wata harkar kasuwanci kuma ta bi ta Uganda ne a farkon watan Oktoba. Ma’aikatar ta ce babu wata alama da ta nuna a lokacin da take Uganda, amma an fara samun alamun cutar ne bayan ta iso Nijeriya.

A cewar sanarwar, kasancewar matar ta yi jigila tsakanin DRC zuwa Nijeriya ta Uganda ba shi ke nuna a Uganda ta kamu da cutar ba, inda ta ƙara da cewa ana cigaba da gudanar da bincike domin gano ainihin gurin da ta kamu da cutar. Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, “gwamnatin Nijeriya ba ta fitar da cikakken bayani akan tafiyarta ba da kuma rahoton lafiya da za su taimaka wa aikin faɗaɗa bincike da ko akwai inda za a bi diddigi,” kamar yadda ma’aikatar ta bayyana.

Gwamnatin Uganda ta ce tana ƙoƙarin taƙaice zirga-zirgar harkokin jinƙai da difulomasiyya, sannan za ta ƙarfafa ayyukan tantancewa da gudanar da lamuran kiwon lafiyar al’umma a kowace mashigar ƙasar, tana mai kira ga al’umma da su kasance masu lura da tare da kiyaye sharuɗɗan wanke hannu da tsaftace muhalli akai-akai. Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da ɓullar cutar Ebola a Birnin Tarayya Abuja.

A ranar Talata ne dai Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da ɓullar cutar a karon farko a Abuja bayan an gano cewa wata mata da ta zo Nijeriya daga Uganda tana ɗauke da ita. Ministan Lafiya da Walwalar Al’umma, Farfesa Ali Pate, wanda ya sanar da labarin, ya ce an gano wasu mutane 44 da ke ɗauke da alamun cutar, waɗanda aka ware su kuma ake kula da su, ciki har da ma’aikatan lafiya, marasa lafiya, masu aikin raino da wasu mutanen da ake zargin sun shigo Nijeriya tare da matar.

By Babaji

Leave a Reply