Rashin cika ƙa’idar mulki ya hana bai wa tsohon gwamnan Kebbi kuɗin barin aiki – Gwamnatin Kebbi

Spread the love

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR Birnin Kebbi

Gwamnatin jihar Kebbi ta kafa hujja da sassan kundin tsarin mulkin Najeriya, da su ne dalilin da tsohon gwamnan jihar, Abubakar Musa Garkuwan Yauri, bai samu kuɗaɗen barin aiki ba, watau fensho da giratuti.

Gwamnatin na raddi ne akan zargin da tsohon gwamnan ya yi cewar an riƙe mashi kuɗaɗen shi, ba’a biyan sa.

Da yake yi ma manema labarai jawabi a Birnin Kebbi, kwamishinan yaɗa labarai da al’adu Yakubu Ahmed Birnin Kebbi, cewa ya yi, Abubakar Musa ya hau karagar mulki a matsayin Gwamnan Kebbi daga watan Janairu 1992 zuwa watan Nuwamba 1993, adadin watanni ashirin da biyu.

Ya ce wannan adadin ya kasa cika ƙa’idar mafi ƙarancin wa’adi na shekara biyu ƙarƙashin dokar da ta shar’anta cewar duk wani tsohon gwamna sai ya cika shekaru biyu cif-cif akan mulki sannan ya kai munzalin karɓar kuɗin fensho da giratuti.

Yakubu ya ci gaba da cewar a watan Fabrairu 2010, hukumar rabon arziki ta ƙasa, (RMAFC), ta rubuta takarda zuwa ga Gwamnan Kebbi da kuma kakakin majalisar dokokin jihar da suke akan mulki na wannan lokacin, ta umurcesu da su bai wa gwamnoni da mataimakan gwamna, kuɗaɗen barin aiki na fensho da giratuti idan sun cika ƙa’ida da wa’adi kamar yadda sashi na 84(5) da kuma sashi na 124(5) na kundin tsarin mulki na Najeriya na shekarar 1999 suka yi tanadi.

Kwamishinan ya ce wannan dokar ta ƙayyade cewar umurnin ya shafi gwamnoni ne da mataimakan su waɗanda sukayi mulki daga shekarar 1999 zuwa shekarar 2003.

Ya ce yaƙini yake cewar dokar ba ta haɗa da waɗanda sukayi mulki daga shekarar 1991 zuwa shekarar 1993 ba, sannan kuma dokar ba daga shekarun baya ta fara aiki ba, ta fara aiki ne daga shekarar da aka ɓullo da ita a 1999.

Yakubu ya sanar da cewar duk gwamnatocin da suka wuce kafin zuwan gwamnati mai-ci-yanzu a jihar Kebbi, sun dogara ne a tanaje-tanajen kundin tsarin mulki, ba su sanya Abubakar Musa ba cikin mai karɓar kuɗin fensho da giratuti da makamantan alawus.

Kwamishinan ya ce, duk da yadda wannan dokar ta gindaya sharaɗi, Gwamna Nasir Idris ya wanzar da nuna tausayi da kyautatawa ga tsohon gwamnan, saboda irin na shi gudunmawar da ya bayar wurin ci gaban jihar Kebbi, sannan ya na darajjashi a matsayin sa na dattijo mai faɗa-a-ji.

Ya ce sau biyu lokuta dabam-dabam, gwamnatin jihar Kebbi ta ɗauki nauyin kai Abubakar Musa Kasar Misrah (Egypt) domin kula da lafiyarshi.

Haka kuma, a lokutan bukukuwa kamar watan Ramadan da Eid-el-Fitr da Eid-el-Kabir da sauran lokuta, Gwamna Nasir Idris yana masa ihsani na kuɗi da kayayyaki.

Bai tsaya nan ba, Kwamred Nasir Idris ya kuma sanya ma wani ɗakin-taro da ke gidan gwamnati sunan Abubakar Musa a shekarar 2025 domin karramashi, sannan kuma ya yi ruwa-da-tsaki wurin naɗa dan tsohon gwamnan a matsayin jakadan Nijeriya ƙwararre, da nufin ci gaba da wanzar da zumumci da kuma karramawa ga tsohon gwamnan da kuma iyalinshi.

Dangane da zargin da ya yi cewar ya kasa tuntuɓar gwamnan, sannan kuma shi gwamna Idris bai tuntuɓeshi ba, Kwamishinan ya fayyace cewar a lokacin zaɓen 2023, Kwamred Idris shi da kanshi ya tafi wurin Abubakar Musa ya shaida mashi cewar ya son ya tsaya takaran gwamnan jihar Kebbi, kuma ya zo ne ya nemi tubarraki da goyon baya da addu’ar tsohon gwamnan, amma Abubakar Musa ya kauda fuska, saboda shi ɗan PDP ne.

Kwamishinan ya ce, tun daga wancan lokacin, tsohon gwamnan ya ƙi ya yi hulɗa da gwamnati.

Amma a lokuta sau biyu ko fiye da haka, manyan muƙarraban gwamnati, sannan kuma da wani ayari na jami’an ‘yan jaridan gwamnati, wanda shi kwamishinan ya jagoranta, sun kai ma Abubakar Musa ziyara a gidanshi da ke Kaduna, suka isar ma sa da saƙon fatan alkhairi da sada-zumunci daga Gwamna Nasir Idris.

Yakubu ya ce an yi hakane domin wanzar da kyakkyawar dangantaka da hulɗa ta ‘yan’uwantaka, amma tsohon gwamnan, Abubakar Musa bai mai da ma gwamna Idris da gwamnatinsa irin wannan karimci ba.

By ukarofi

Leave a Reply