Ƙungiya ta buƙaci INEC ta yi bayani kan cire Pantami, Gwarzo daga jerin ’yan takara

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

Ƙungiyar National Association of Achievers Movement (NAAM) ta buƙaci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta yi bayani kan cire wasu ’yan takarar gwamnan jihohi, ciki har da Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, Ladi Adebutu da Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, daga jerin sunayen ’yan takarar da ta fitar na zaɓen 2027.

Ƙungiyar ta kuma nuna shakku kan daidaiton matakan da hukumar ke ɗauka, inda ta buƙaci ta bayyana dalilin da ya sa aka cire wasu ’yan takara, yayin da aka saka wasu a jerin sunayen duk da cewa tsarin tsayar da su takara ya fuskanci tambayoyi daga jama’a.

Da yake magana da manema labarai a Gombe, shugaban ƙasa na NAAM, Bishop Fumlack Victor, ya ce cire sunayen ’yan takarar ya haifar da damuwa kan ko ana amfani da dokokin zaɓe iri ɗaya ga kowa da kuma ko tsarin tsayar da ’yan takara yana tafiya cikin gaskiya da riƙon amana.

Ya ce INEC ta danganta cire sunayen da rashin bin ƙa’idojin gabatar da rajistar ’ya’yan jam’iyya, kamar yadda sashe na 77(5) da 77(7) na dokar zaɓe ta 2026 suka tanada, bisa hukuncin kotun ƙoli da aka yanke ranar 24 ga Satumba, 2026.

Sai dai Victor ya tambayi ko an yi amfani da wannan ƙa’ida ga dukkan ’yan takara ba tare da nuna bambanci ba.

Ya kawo misalan Sanata Shehu Buba na Jam’iyyar PRP a Bauchi, tsohon Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Adamu, mai ritaya, na Jam’iyyar SDP a Nasarawa, da Hon. Kingsley Chinda na Jam’iyyar APC a Rivers.

A cewarsa, Sanata Buba ya zama ɗan takarar gwamnan PRP ne bayan sauya sheƙa daga APC, a lokacin da ake taƙaddama kan zaɓen fidda gwani na jam’iyyar a Bauchi.

Ya kuma yi tambaya kan lokacin da Chinda ya yi rajista da APC da kuma lokacin da ya fice daga Jam’iyyar PDP.

Haka kuma, ya ce an samu rahotannin cewa Mohammed Adamu ya zama ɗan takarar SDP a Nasarawa ne bayan janye sunan wani ɗan takara da aka fara tsayarwa da kuma gudanar da tsarin sauya sunan ɗan takara.

Shugaban NAAM ya jaddada cewa ƙungiyar ba ta neman a cire duk wani ɗan takara da INEC ta amince da shi, sai dai tana son hukumar ta yi cikakken bayani kan dalilai na doka da hujjojin da suka sa ta ɗauki waɗannan matakai.

“Babbar tambayarmu ita ce, idan an cire wasu ’yan takara saboda rashin cika ƙa’idojin rajistar ’ya’yan jam’iyya da doka ta tanada, wane dalili na doka da hujja ne ya sa aka amince da wasu ’yan takara waɗanda tsarin tsayar da su ma ya jawo tambayoyi?” in ji shi.

Victor ya buƙaci INEC ta bayyana ko rajistar ’ya’yan PRP da ke ɗauke da sunan Buba an miƙa ta cikin lokacin da doka ta kayyade.

Ya kuma nemi ta yi bayani kan ko an cika ƙa’idojin rajistar ’yan jam’iyya da na tsayar da ’yan takara a shari’o’in Chinda da Adamu.

Dangane da Pantami, ya ce ya kamata INEC ta bayyana dalilin da ya sa ta cire sunansa, musamman ganin cewa ya lashe sabon zaɓen fidda gwani na PDP a Gombe bayan an yi shari’o’i kan tsarin tsayar da ɗan takarar jam’iyyar a baya.

Ya ce hukumar ta kuma fayyace yadda sakamakon sabon zaɓen fidda gwanin ya shafi ƙa’idojin doka da suka shafi rajistar ’ya’yan jam’iyya.

Ƙungiyar ta buƙaci INEC ta fitar da cikakken bayani kan cire ’yan takara a jihohin Gombe, Ogun da Kano, tare da bayyana dalilan doka da matakan da ta bi wajen amincewa da ’yan takara a Bauchi, Nasarawa da Ribas.

Victor ya ce NAAM ba ta neman a dawo da sunayen Pantami, Adebutu da Gwarzo kai tsaye cikin jerin ’yan takara ba tare da bin ƙa’idojin doka ba, haka kuma ba ta neman a cire waɗanda tuni hukumar ta amince da su.

“Ba mu neman a cire Sanata Buba, Hon. Chinda, IGP Adamu ko wani ɗan takara da sunansa ke cikin jerin INEC. Haka kuma, ba mu neman a dawo da sunayen Farfesa Pantami, Mista Adebutu, Kwamared Gwarzo ko wani ɗan takara da aka cire ba tare da yin binciken doka da ya dace ba.

“Abin da muke buƙata shi ne a yi amfani da ƙa’ida guda wajen tabbatar da bin doka, adalci a matakai da kuma daidaita yadda ake mu’amala da dukkan ’yan takara,” in ji shi.

Ya buƙaci INEC ta yi bayanin matsayarta cikin lokaci, sannan ya shawarci ’yan takarar da abin ya shafa da jam’iyyunsu da su bi hanyoyin shari’a da na gudanarwa da doka ta tanada kafin wa’adin da aka ƙayyade ya cika.

Ya ƙara da cewa amincewar jama’a da zaɓen 2027 za ta dogara, a wani ɓangare, da yadda hukumar za ta tabbatar da adalci, daidaito da gaskiya wajen gudanar da harkokin tsayar da ’yan takara.

By ukarofi

Leave a Reply