Kotu ta yi wa mai tsegumin ɗan bindiga Gana ɗaurin shekara 40 kan ba shi bayanan zirga-zirgar jami’an tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Alhamis, 22 ga Oktoba, 2026, Babbar Kotun Tarayya a Abuja da yanke wa Sunday Frank hukuncin zaman gida yari na tsawon shekaru 40 bayan ya amsa laifin cewa ya yi aiki a matsayin mai tsegumi ga marigayi ɗan bindigar Benuwai, Terwase Akwaza, wanda aka fi sani da Gana.

Rahotanni sun bayyana cewa, Gana, wanda ya fara a matsayin mamban wata ƙungiyar mayaƙa da ke kare ƙauyukan Jihar Benuwai daga hare-haren wasu da ake zargin makiyaya ne, an halaka ke shi ne a watan Satumban 2020.

A bayanan kotu, Fank, wanda ainihinsa dan Ƙaramar Hukumar Katsina-Ala ne ta Jihar Benuwai, an gabatar mata da wasu tuhume-tuhume guda huɗu akansa, waɗanda daga ciki Gwamnatin Tarayya ta tuhume shi da kasancewa mai sanya ido da bayar da bayanan zirga-zirgar jami’an tsaro ga Gana. Haka kuma, gwamnatin ta yi zargin cewa ayyukan da Frank yake yi a madadin Gana sun faɗaɗa daga Jihar Benuwai zuwa Jihar Taraba.

Musamman, ƙarar, wadda Antoni Janar na Ƙasa (AGF) kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN) ya shigar, ta zargi mai laifin da yin garkuwa da wani mai suna Samuel a shekarar 2022 kuma ya riƙe shi har sai da aka biya fansar N40,000 domin sako shi. An kuma zargi Frank da aikata laifukan da sun ci karo da Sashe na 21 da 24 na Haramtawa da Kariya ga Ayyukan Ta’addanci ta 2022.

Duk da cewa mai laifin ya musanta tuhuma ta ɗaya, biyu da ta uku waɗanda suka alaƙanta shi da hannu a garkuwa, ya amsa laifin cewa shi mai tsegumi ne ga marigayin ɗan bindigar, wato tuhumar ta huɗu. Ganin haka ya sa AGF ɗin ya nemi kotun da ta yi watsi da tuhume-tuhume ukun da wanda ake zargin ya musanta. Kotun ta amince da hakan bayan ta kira alƙalin da ya kasance ɗaya daga cikin tawagar da suka yi bincike akan Frank ya tabbatar da haka.

An kama Frank ne a shekarar 2022 kan hannu a hulɗa da Gana wajen samar masa da bayanan jami’an tsaro, sannan wani shaida a kotun ya ce an samu Frank da hannu a ayyukan ‘yan bindiga da garkuwa da wasu mutum biyu. Bayan haka ne Mai Shari’a Hawa Yilwa ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 40 a kurkuku, wanda zai fara aiki daga ranar da aka kama shi. Kotun ta kuma bayar da umarnin an garzaya da shi gidan gyaran hali bayan kammala zamansa a gidan yari.

By Babaji

Leave a Reply