Ku yi duk abinda za ku yi domin ganin Tinubu ya ci zaɓe – Tompolo

Spread the love

Mai faɗa aji Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo, ya buƙaci shugabannin ƙungiyar ‘PBAT Door-to-Door Movement’ da su yi aiki tuƙuru domin tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Tompolo, wanda shi ne babban mai ɗaukar nauyin ƙungiyar, ya buƙaci ‘yan ƙungiyar da su bi lungu da saƙo dan ganin an wayar da kan al’umma zaɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu.

Tompolo ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke miƙa motoci guda 26 da kuma ƙaddamar da masu gudanar da ƙungiyar a jihar Gombe.

Haka kuma, masu gudanarwar sun karɓi wasu kayan aikin yaƙin neman zaɓe daban-daban.

Tompolo, wanda babban daraktan kamfanin Tantita Security Services Limited, Chief Kestin Pondi, ya wakilta, ya buƙaci masu gudanarwar da su yi aiki tuƙuru dan ganin samun nasarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu.

A nasa jawabin, Gwamna Yahaya, wanda ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa jam’iyyar APC za ta yi nasara a jihar Gombe tare da goyon bayan sake zaɓen Tinubu, ya ce manufofin shugaban ƙasar sun samar da damammaki don raya ababen more rayuwa da bunƙasa fannin noma.

By ukarofi

Leave a Reply