Makaranta ya kamata ta kasance mafakar ilimi, gano baiwa da gina kyakkyawar makoma, ba wurin da masu aikata laifuka ke farautar yara ba. Sai dai a sassa daban-daban na Nijeriya, ƙara yaɗuwar garkuwa da ɗalibai na mayar da azuzuwa wuraren fargaba, yayin da jarrabawa ke zama abin da ke ƙara tsoratar da ɗalibai maimakon zama wata dama ta tabbatar da abin da suka koya.
Bayan mummunan abin da ke tattare da sace mutum, akwai wata illa da ba ta bayyana kai tsaye, amma take da matuƙar muni: raunin da lamarin ke haifarwa a zukatan yara, wanda ke shafar karatunsu, yarda da kansu da kuma makomarsu. Rashin tsaro abin damuwa ne tun farko, amma illolinsa na dogon lokaci ga tunanin yara da ɗaliban da ke shirin jarrabawa na iya kassara ƙoƙarinsu a karatu tare da kawo cikas ga ci gaban rayuwarsu.
Masu ɗauke da makamai da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya na ci gaba da kai hare-hare kan makarantu, musamman a yankunan da ba su da isasshen kariya. Suna sace ɗalibai da malamai domin neman kuɗin fansa ko wasu dalilai na laifi. Illar waɗannan hare-hare ba ta tsaya ga al’ummomin da aka kai wa hari kaɗai ba; tana shafar ƙasar baki ɗaya.
ƙungiyar agaji ta Save the Children International ta fitar da alƙaluman da ke nuna girman matsalar. A cewar ƙungiyar, an samu aƙalla hare-haren sace ɗalibai guda 10 a sassan Nijeriya tsakanin Janairun 2024 da Nuwamban 2025, inda kusan yara 670 suka shiga cikin lamarin.
A watan Mayun 2026, wasu ’yan bindiga sun kai hari kan makarantu a ƙaramar hukumar Oriire ta Jihar Oyo, inda suka yi awon gaba da ɗalibai da malamai. An samu nasarar kuɓutar da mutum 44 daga cikin waɗanda aka sace a ranar 10 ga Yuli, bayan shafe kwanaki 56 a hannun masu garkuwa da mutane. Sai dai malamai biyu sun rasa rayukansu a yayin wannan mummunan al’amari.
Haka kuma, hare-haren da aka kai a yankin Askira-Uba na Jihar Borno a watan Satumban 2026 sun yi sanadin kasancewar kusan ’yan makaranta 44 a hannun masu garkuwa da mutane, kamar yadda rahotanni suka nuna. Hare-haren sun kuma tilasta rufe wasu makarantu, lamarin da ya hana sauran yara damar ci gaba da karatunsu.
Abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda ɗaliban da ke shirin rubuta jarrabawar Hukumar Shirya Jarrabawar Afirka ta Yamma (WAEC) da ta Majalisar Jarrabawa ta ƙasa (NECO) ke fuskantar barazanar cewa makarantu na iya zama wuraren da za a kai musu hari.
A watan Yunin 2026, wasu ’yan bindiga sun sace ɗaliban da ke rubuta jarrabawar NECO a wata makarantar sakandare da ke Lassa, a yankin Askira-Uba. Kasancewar wurin da ya kamata ɗalibai su rubuta jarrabawa cikin kwanciyar hankali ya zama wurin sace mutane ba ƙaramin abin takaici ba ne. Wannan lamari ya nuna gazawar matakan tsaron makarantu da kuma yanayin tsaron ƙasa baki ɗaya.
ɗalibin da kullum yake cikin fargabar yiwuwar kai hari ba zai iya mai da hankali ga karatu cikin nutsuwa da kwarin gwiwar da ake buƙata domin samun nasara ba. Ko yaran da ke ci gaba da zuwa makaranta na iya kasancewa a zahiri a cikin aji, amma hankalinsu yana can nesa, yana ta fama da fargaba, tunanin abubuwan tashin hankali da damuwar lafiyarsu.
Ga wasu yaran kuwa, tsoron ya kai matakin da suke ƙin zuwa makaranta. Iyaye da suka damu da lafiyar ’ya’yansu ba za a zarge su ba idan suka yanke shawarar tsare su a gida domin kare su daga haɗari.
Rufe makarantu akai-akai da ɗaukar tsawon lokaci ba tare da zuwa makaranta ba na ƙara faɗaɗa giɓin ilimi tsakanin yara, yana ƙara yiwuwar barin karatu da wuri, tare da rage damar kammala karatunsu.
Illar matsalar ba ta tsaya ga sakamakon jarrabawa kaɗai ba. Yaran da suka fuskanci garkuwa da mutane da sauran nau’o’in tashin hankali na iya fama da mafarkai masu tayar da hankali, fargaba marar yankewa, baƙin ciki, nisantar jama’a da kuma matsalar kwaciyar hankali.
Waɗanda abin ya shafa kai tsaye na buƙatar kulawar ƙwararru ta fuskar lafiyar kwakwalwa domin su sake samun kwanciyar hankali da jin cewa suna cikin aminci. Idan ba a ba su kulawar da ta dace ba, raunin da suka samu a zukatansu na iya lalata dangantakarsu da sauran mutane, kawo cikas ga ci gaban zamantakewarsu da kuma hana su sake amincewa da wasu.
Wane irin zamani muke shirin ginawa idan yara suka fara danganta makaranta da haɗari maimakon dama ta samun ci gaba? Al’ummar da ta taso cikin fargaba na iya rasa kwarin gwiwa, juriya da burin cimma manyan manufofin da ake buƙata domin yin gogayya a duniyar yau.
Rashin kyakkyawan sakamako a karatu na iya hana yara samun guraben karatu a manyan makarantu, ayyukan yi da sauran damammaki. Haka kuma, raunin yarda da kai na iya sa yara masu baiwa su fid da rai, su bar bin burinsu tun kafin su kai ga cimma shi.
Illar wannan matsala ba ta tsaya ga ɗalibai da iyalansu kaɗai ba; tana shafar al’umma da ƙasa baki ɗaya. Duk yaron da aka hana damar amfani da baiwarsa yadda ya kamata na iya zama wata dama da ƙasa ta rasa a fannonin kimiyya, likitanci, fasaha, aikin gwamnati, kasuwanci da sauran ɓangarorin ci gaban ƙasa.
Baiwar da Allah Ya ba wa yara na iya kasancewa a ɓoye ba tare da an amfana da ita ba. Al’ummomi na iya rasa shugabannin gobe, yayin da ƙasa za ta iya fuskantar ƙarancin ƙwararrun ma’aikata masu ilimi, ƙwarewa da kwarin gwiwar taimakawa wajen gina ta.
Haka kuma, idan aka yi watsi da matsalolin da suka shafi lafiyar kwakwalwar yaran da abin ya shafa, hakan na iya ƙara tsananta matsalolin zamantakewa da raunana haɗin kan al’umma.
Saboda haka, gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi, hukumomin tsaro, shugabannin makarantu, iyaye da al’ummomi dole ne su fahimci cewa kare ilimi ya wuce yin Allah-wadai da hare-hare bayan sun faru.
Ana buƙatar inganta tattara bayanan sirri, gaggauta kai ɗauki idan an samu barazana, tabbatar da tsaron makarantu, samar da tsarin gargaɗin wuri da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da al’ummomin yankunan da ke cikin haɗari.
Makarantun da ke fuskantar barazana suna buƙatar ingantaccen binciken haɗarin tsaro, hanyoyin fitar da zalibai cikin gaggawa idan an kai hari, tsarin sadarwa na gaggawa da kuma ma’aikatan tsaro da suka samu horon da ya dace.
A duk lokacin da aka samu sahihan bayanan sirri da ke nuna akwai yiwuwar kai hari, hukumomi su ɗauki matakan kariya tun kafin faruwar lamarin. Amma ya kamata a tabbatar cewa waɗannan matakan ba su zama sanadin hana yara damar samun ilimin da suke da haƙƙinsa na dindindin ba.
Yaran da aka kuɓutar daga hannun masu garkuwa da iyalansu ya kamata su samu ƙwararrun masu ba da kulawar lafiyar kwakwalwa da shawarwari. Haka kuma, makarantu suna buƙatar tallafi da kayan aikin da za su taimaka wajen dawo da yaran da suka shiga tashin hankali cikin aminci, bayan an ba su shawarwarin da suka dace tare da tantance halin da suke ciki.
Nijeriya ba za ta iya ɗaukar sace ’yan makaranta a matsayin wani abu na yau da kullum ba. Kowace rana da yara suka shafe ba tare da zuwa makaranta ba, kowace jarrabawa da suka rubuta cikin fargaba da kuma kowane iyaye da aka tilasta wa zaɓi tsakanin tsaron ’ya’yansu da neman iliminsu, duk suna ƙara jefa makomar ƙasar cikin rashin tabbas.
Ainihin ma’aunin tsaron ƙasa ba wai kawai rashin jin ƙarar harbe-harbe a birane ba ne. Babbar tambayar ita ce: shin yaro zai iya fita daga gidansa ya shiga aji cikin kwanciyar hankali, yana da yaƙinin cewa zai dawo gida lafiya?
’Ya’yanmu sun cancanci samun ilimi ba tare da fargabar ta’addanci ba. Kare su nauyi ne da ya rataya a wuyan ƙasa baki ɗaya.
Idan muka gaza tabbatar da tsaron makarantu da warkar da raunin da ke cikin zukatan yaranmu, muna fuskantar haɗarin sadaukar da yarintarsu da kuma makomar Nijeriya baki ɗaya.
