Rashin tsaro: Manazarci ya caccaki Gwamna Lawal kan matsayar rashin tattaunawa da ‘yan bindiga a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Wani manazarci kan al’amuran jama’a, Abdulrasheed Buhari Yandi, ya koka kan taɓarɓarewar tsaro a Jihar Zamfara, inda ya zargi Gwamna Dauda Lawal da rashin ɗaukar mataki duk da maimaita matsayarsa na ƙin tattaunawa da ‘yan bindiga.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis a Gusau, Yandi ya jajanta wa iyalan waɗanda aka kashe, aka sace da kuma waɗanda suka rasa muhallansu a hare-haren baya-bayan nan da suka faru a Bukuyum, Gwashi, Dansadau da Bindin, inda ya bayyana cewar an kashe tare da sace mutane sama da 150.

A cewarsa, al’ummomi na cikin hatsari, inda ‘yan bindiga ke iƙirarin mamaye wasu yankuna tare da tilasta wa mazauna biyan haraji na haram ga miyagun laifuka domin su tsira.

Ya koka kan yadda wasu manyan hanyoyi da suka haɗa da Gusau-Dansadau da Mayanchi-Anka-Gummi suka zama tarkon mutuwa, lamarin da ya durƙusar da zirga-zirga da harkokin tattalin arziki.

Ya bayar da hujjar cewa kin tattaunawa rabin dabara ne kawai, ɗayan rabin kuma shine ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki na murƙushe ‘yan bindigan, wanda ya ce babu shi.

Yandi ya yi ƙarin haske cewa ba yana goyon bayan a yi sulhu da miyagu bane, sai dai yana neman kariya ga ‘yan ƙasa.

Ya yi kira ga Gwamna Lawal da ya wallafa cikakken tsarin tsaro wanda ya haɗa da tsare hanyoyin Gusau-Dansadau da Mayanchi-Anka-Gummi, dawo da tsaron al’umma da tattara bayanan sirri, haɗin kai mai inganci da hukumomin tsaro na tarayya, bayyana yadda ake kashe kuɗaɗen tsaro cikin gaskiya, da kuma bayar da agajin gaggawa ga al’ummomin da suka rasa muhallansu.

Ya koka cewa al’ummar Zamfara sun gaji da binne ‘yan uwansu, biyan kuɗin fansa da barin gidajensu.

A cewarsa, matsayin ƙin tattaunawa da ‘yan ta’adda bai hana kashe-kashe, garkuwa da mutane da karɓar haraji da ‘yan ta’adda ke yi ba.

By ukarofi

Leave a Reply