2027: Ku faɗi gaskiyar halin da ƙasa ke ciki – Sarkin Katsina ga tawagar Tinubu

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya buƙaci jam’iyyar APC da shugabanninta da su faɗi gaskiya game da halin da Najeriya ke ciki, maimakon yaudarar al’umma, musamman dangane da matsalar tsaro da ƙalubalen tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta.

Sarkin ya bayyana hakan ne yayin da Sanata Abdulaziz Abubakar Yari, darakta-janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaba Bola Ahmed Tinubu na shekarar 2027, ya kai masa ziyara a fadarsa da ke jihar Katsina.

A yayin ziyarar, Sarkin ya jaddada cewa matsalar rashin tsaro na ci gaba da shafar rayuwar al’umma, inda manoma da dama ke fuskantar matsaloli wajen zuwa gonakinsu domin gudanar da ayyukan noma.

Ya kuma nuna damuwa kan matsin tattalin arziki da ke ƙara tsananta wa jama’a, lamarin da ke buƙatar a faɗi gaskiya game da halin da ake ciki tare da ɗaukar matakan da za su taimaka wajen sauƙaƙa wa al’umma wahalhalun rayuwa.

Jawabin Sarkin ya zo ne a daidai lokacin da ‘yan siyasa ke shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

By ukarofi

Leave a Reply