Ebola: Ka da ’yan Nijeriya su ɗaga hankalinsu — Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Lafiya, Dokta Muhammed Ali Pate, ya buƙaci ’yan Najeriya da ka da su ɗaga hankalinsu game da cutar Ebola da ta ɓulla a Abuja, inda ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya tana ɗaukar matakan daƙile yaɗuwar cutar.

Pate, ya bayyana hakan ne a fadar shugaban ƙasa a ranar Laraba, bayan ganawarsa da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila.

Tun da farko, ministan ya tabbatar da cewa wata mata da ta shigo Nijeriya ta jirgin sama daga ƙasar Uganda ta kamu da cutar Ebola, bayan amma ana yi mata magani a wani asibiti mai zaman kansa a Abuja.

Da yake magana da manema labarai a fadar shugaban ƙasa, Pate, ya ce Nijeriya tana aiki tare da Uganda da sauran hukumomin lafiya domin shawo kan cutar.

Ya ce, “Mun gano mutum ɗaya da ta kamu da cutar. Muna bin diddigin mutanen da suka yi mu’amala da ita, tare da ɗaukar matakan daƙile yaɗuwa cutar.

“Gwamnatin Tarayya tana da ƙwararrun hukumomin da za su iya shawo kan wannan matsala. Mun yi nasarar shawo kan irin wannan yanayi a shekarar 2014, kuma muna da ingantattun cibiyoyin kula da lafiyar jama’a. Ya kamata ’yan Najeriya su kwantar da hankalinsu.”

Pate, ya buƙaci ’yan Nijeriya da su kasance cikin shiri, su bi shawarwarin lafiya daga sahihan majiyoyi, sannan su guji yaɗa labaran ƙarya.

Ya ce Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC) tana aiki dare da rana, tare da goyon bayan kwamitin da aka kafa domin kula da lamarin.

Ministan, ya yi gargaɗin cewa ka da jama’a su firgita, yana mai cewa cutar ta shigo ne daga ƙasashen waje kuma gwamnati tana ƙoƙarin shawo kanta.

Ya ƙara da cewa, “Idan yanayin ya sauya, za mu sanar da ’yan Nijeriya.”

By ukarofi

Leave a Reply