Za a taka wa masu gidajen haya burki

Spread the love

*Yadda Majalisar Wakilai za ta hana karɓar kuɗin fiye da na shekara guda

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Majalisar Wakilai ta Nijeriya na nazarin wani ƙudirin doka da ke neman hana masu gidaje, masu kula da kadarori da dillalan gidaje a Babban Birnin Tarayya, Abuja, tilasta wa ’yan haya biyan kuɗin haya na sama da watanni 12 a matsayin sharaɗin shiga sabon gida ko sabunta yarjejeniyar haya.

Shi ƙudirin, wanda ’yan majalisa Paul Nnamchi, mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Enugu ta Gabas/Isi-Uzo, da Ahmed Doro, mai wakiltar mazaɓar Bindawa/Mani a Jihar Katsina suka gabatar, yana da nufin kafa hukumar da za ta kula da tsarin biyan kuɗin haya tare da kare haƙƙin ’yan haya daga cin zarafi.

ƙudirin ya kuma tanadi matakan da za su hana masu gidaje kauce wa wannan doka ta hanyar amfani da dillalai, ƙaƙaba kuɗaɗen hidima, ƙirƙirar sabbin yarjejeniyoyin haya ba bisa ƙa’ida ba, raba yarjejeniya zuwa sassa ko amfani da wasu dabaru domin tilasta wa ’yan haya biyan kuɗin haya na fiye da shekara guda gaba ɗaya.

Sai dai ƙudirin ya bayyana cewa ba za a hana ɗan haya biyan kuɗin haya na sama da shekara guda ba idan shi da kansa ya zaɓi yin hakan bisa raɗin kai, ba tare da an tilasta masa, yi masa barazana, nuna masa wariya ko ɗaukar matakin ramuwar gayya ba. Haka kuma, dole ne a rubuta yarjejeniyar da biyan kuɗin a hukumance.

Bugu da ƙari, kudirin ya buƙaci masu gidaje da wakilansu su bai wa ’yan haya yarjejeniyar haya a rubuce kafin fara zama a gidan ko kuma a lokacin fara zaman. Yarjejeniyar za ta ƙunshi adadin kuɗin haya, tsarin biyan kuɗi, tsawon lokacin haya, kuɗin ajiya da za a mayar, ƙarin kuɗaɗe, da haƙƙoƙi da nauyin da ke kan kowane ɓangare.

ƙudirin ya tanadi kafa Hukumar Kula da Dokokin Haya da Kare Haƙƙin ’Yan Haya ta Babban Birnin Tarayya, wadda za ta binciki koke-koke, sa ido kan bin doka, taimakawa wajen sasanta rikice-rikicen haya da kuma ba da umarnin mayar da kuɗaɗen da aka karɓa ba bisa ƙa’ida ba.

Idan hukumar ta gano cewa an tilasta wa ɗan haya biyan kuɗin haya saɓanin abin da dokar ta tanada, za ta iya umartar a mayar masa da kuɗin da aka karɓa ba bisa ƙa’ida ba cikin kwanaki 30 daga ranar da aka miƙa umarnin.

Dangane da hukunci, ƙudirin ya tanadi tara daga naira 500,000 zuwa Naira miliyan biyar ga duk mutumin da aka samu da laifin karya dokar biyan haya gaba, da sanin cewa hakan ya saɓa wa doka. Kamfanonin da suka aikata irin wannan laifi kuwa za su fuskanci tara daga naira miliyan biyar zuwa miliyan 20.

Haka kuma, duk wanda aka samu da laifin ƙin bin ingantaccen umarnin gyara da hukumar ta bayar, zai iya fuskantar tarar da ta kai naira miliyan ɗaya. ƙudirin ya tabbatar da cewa ’yan haya da masu gidaje za su ci gaba da samun damar neman adalci a kotu. Haka kuma, duk wanda bai gamsu da hukuncin hukumar ba zai iya ɗaukaka ƙara zuwa Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya cikin kwanaki 30.

A bara, Majalisar ta kuma gabatar da shawarar takaita ƙarin kuɗin haya a faɗin Nijeriya zuwa kashi 20 cikin ɗari, tare da kira ga Gwamnatin Tarayya da ta tabbatar da aiwatar da matakin. Sai dai har yanzu ba a samu tabbataccen bayani da ke nuna cewa an aiwatar da wannan shawara ba.

By ukarofi

Leave a Reply