Kano: Yadda jaridar Triumph da KPP ke neman rasa madafa

Spread the love

Daga MUSTAPHA IBRAHIM TELA a KANO 

Kamfani ko hukumar KPP, wato Kano Printing Press, an kafa ta ne a shekara ta shekara ta 1938 a matsayin kamfani ko hukuma ta gwamnati mai aikin ɗab’i na buga takardun gwamnatin Kano, littatfai da sauransu, har ma da na kamfanoni masu zaman kansu da ɗaiɗaikun jama’a da sauransu, kuma haka abin yake a yanzu.

Sai kuma jaridar Triumph , wacce tsohon Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi ya kafa ta a shekarar 1980 da manufar samar da kafar yaɗa labarai mai karfi ta gwamnatin jiha, domin isar da saƙonni ga al’umma da kuma isar da saƙon al’umma da ra’ayoyinsu ga gwamnati da kuma faɗar gaskiya ko akan waye daidai da ƙa’idojin aikin jarida a ƙarƙashin doka na kundin tsarin mulkin ƙasa a rubuce, kamar yadda muka karanta a makarantar koyan aikin jarida a matakin farko har zuwa matakin karato na biyu a jami’a. Kuma babban kirarin jaridar Triumph da ya yi shuhura shine, ‘Idan Za Ka Faɗi, Faɗi Gaskiya Komai Taka Ja Maka Ta Biya, Inji Editanmu Na Gaskiya Wacce Ta Fi Dubun Zinariya’.

Kuma harkar ɗab’i, wato wallafa rubuce-rubuce, ita ce tushen cigaban al’umma da duniya bakiɗaya, domin ɓacin rubutu da ba mu samu addini ba, da ba mu samu tarihi ba, da ba mu samu littattafai na kimiyya da fasaha ba da ba mu samu littattafai na koyan aikin kiwon lafiya da noma da saura fannoni na cigaban rayuwar ɗan adam ba da dai sauransu ba. 

Kuma masana tarihi sun baiyyana hanyoyin samun tarihi guda uku, wanda ake kira da ‘Source Of History’. Na farko shine abin da aka rubuta, wato ‘Book of Records’; na biyu ‘Archology’, wato abin da aka haƙo daga ƙasa na kayayyakin magabata da suka yi amfani da su, kamar tukwane da sauransu, waɗanda yanzu ake iya ganin su a gidajen adana kayan tarihi da sauran gurare. Sai na uku shine ‘Oral Tradition’, wato samun labarai na dauri daga dattawa magabata.

Bugu da ƙari, masana suka ce amma hanya mafi ƙarfi da inganci ita ce, abin da aka rubuta, kamar yadda malam addini suke cewa, abin da aka rubuta shi ake kiyayewa fiye da abin da aka faɗa a baki, kuma hakan ce ta sanya Bahaushe ke cewa, ‘hali zanen dutse’, wato idan ka yi zane akan dutse, yana nan har sai abin da hali ya yi, to haka rubutu yake.

Wannan a taƙaice kenan da ke nuna mahimancin rubutu tasirinsa da amfaninsa da bai kamata a yi sako-sako ko riƙon sakainar kashi da shi ba, musannan ga al’umma mai manufa da hangen nesa da kuma fatan kyakkyawar makoma ga al’umma ta gobe da jibi da gata.

Wanne hali Hukumar KPP take ciki a yanzu kuma ina makomarta a wajen gwamnatin jihar Kano da ke ƙarƙashin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusif da ake yi mata take da ‘gwamnatin ilimi’?

Bincike dai ya nuna cewa, KPP, wato Kano Printing Press na da sassa da duk ake buƙata wajen samar da ɗab’i na zamani kuma su na da ƙwararrun ma’aikata masu kishin aiki, kamar yadda ya kamata. Wannan kishin ne ma ya sa zuwan Gwambna Abba Kabir Yusif su ka ba shi shawara cewa a gina musu wata cibiya da za su riƙa horar da matasa wannan sana’a ta ɗab’i ta yadda za a sama wa dubban matasa aikin cikin sauƙi kuma Kano ta ci gaba da riƙe kambunta na ‘Ko Da Me Ka Zo An Fi Ka’, kamar yadda sauran fannoni suke a Kano.

Haka kuma bincike ya nuna cewa, gwamna ya ji daɗin wannan buƙata daga Kano Priting Press na a gina wannan cibiya da kuma sama wa wannan maɗaba’a sabbin injina na zamani, kuma ya amince tun a shekarar 2024, amma sai dai kash bincike ya nuna har yanzu dai babu sabbin injinan da ake buƙata na zamani, kuma cibiyar an fara gini ba a kammala ba balle a samu ɗaukar matasa da za a horar da su wannan sana’a mai daraja da uban matasa aikin yi a koi’na cikin duniya.

Haka kuma binciken har ya gano wasu mahimman injina, waɗanda da zarar Gwamna Abba ya sama wa KPP, to shikenan ta zama gagarabadau a harkar ɗab’i ba a Arewa ba, har ma Nijeriya bakiɗaya ko ma Afirka, domin da zarar KPP ta samu wannan injina, to Lagos ma Kano za su garzayo kan harkar ɗab’i da ma jihohi maƙwabtanta. Ga kaɗan daga cikin sunayen injinan, waɗanda ake kira mai fitar da launi 4 ana kiransa ‘Four Units’ da Turanci, akwai mai Launi biyu, ‘Two Units’, akwai mai kala ɗaya, sai kuma waɗanda ake rubutu ko zane a jikin leda, riga, jaka da sauransu.

Haka kuma wani ƙalubale da KPP da take fuskanta shine, yadda sama da kasha 70 na ma’aikatu da hukumomin gwamnatin Kano da ƙananan hukumomi suka bijire wa umarnin da ofishin Sakataran Gwamnatin Jihar Kano ya bayar na su riƙa ba wa KPP duk wani aikin ɗab’i kasancewarta maɗaba’a ce ta gwamnati, wanda ga duk wanda ya san tsarin aikin gwamnati ya san cewa, yin hakan zai bayar da ingantaccen aiki da kare sirrin gwamnati, kuma yaba wa hukumar da gwamnati kuɗin shiga na biya masu aikin wucingadi da na haraji a matakin jiha da tarayya.

Amma duk da umarnin da ke cikin takardar da aka raba wa ɗaukacin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin Kano mai lamba kamar hakan; SSG/AGS/R/66/!!!/57/ da kwanan wata 23 ga Agusta, 2023, kamar yadda binciken Blueprint Manhaja ya nuna, amma masu kai aikin a KPP na ma’aikatun gwamnatin jihar ba su kai kashi 30 ba.

Sai dai kuma duk da bincike a jaridance na hanyoyin doka, kuma mun yi ƙoƙarin jin ta bakin Shugaban Hukumar KPP ko yaya ya kalli wannan bayani, inda Matimakin Shugabar Hukumar KPP, Hon. DMD Adamu Yahya, ya ce, ba shakka gwamna ya yi rawar gani wajen kawo wa hukumar cigaba, kuma lallai sun rubuta takardun buƙatunsu ga Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusif, amma dai har yanzu suna sauraro, kuma suna sa rai da addu’ar zuwan waɗannan kayin aiki a wannan lokaci, domin cigaban Kano da al’ummarta da ma Nijiriya bakiɗaya Yadda KPP ta kasance kenan a taƙaice.

Sai kuma fitacciyar jaridar Triumph . Jarida ce mai ɗimbun tarihi da tasiri aikin jarida a Arewa, Nijeriya, Afika dama duniya bakiɗaya, domin kuwa baya ga kasancewar ta kafar yaɗa labarai, ta kasance wata cibiya babbar jami’a ta samun horo a Nijeriya, inda ta samar da mashahuran ’yan jarida a ƙasar. An kafa Triumph a 1980 a lokacin Marigayi Sarkin Gumal, Ahmed Muhammed Sani na Biyu shine kwamishinan yaɗa labarai na gwamnatin Rimi. Sai dai kuma a zamanin tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa KwanKwaso, ne Triumph ta yi dogon suma, inda aka rufe kamfanin, aka tarwatsa ma’aikiatanta zuwa wasu ma’aikatun irin su, Ma’aikatar Yaɗa Labarai, gidan radiyo Kano, gidan talbijin na Kano, wato ARTV da sauransu. 

Koda yake wata majiya ta tabbatar da cewa, garƙame Triumph ba laifin Kwankwaso ba ne, an zargi shugaban Triumph na lokacin da cewa, shine ya gaza riƙe kamfanin bayan Gwamna Kwankwaso ya yi sa masa sharuɗɗa ya amince na cewa, nawa yake buƙata na kuɗi a ba shi, kuma majiya ta ce shigaban na Triumph na wancan lokacin ya faɗi kuɗin aka ba shi, amma ba a je ko’ina ba kamfanin ya gaza riƙe kansa. Majiyar ta ce, hakan ta fusata Kwankwaso, ya umarci Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida da Wasanni na lokacin, Farfesa Umar Faruk, ya jagoranci garƙame gidan jaridar. Wannan ya faru ne a hawan Gwamna Kwankwaso na biyu daga 2011 zuwa 2015.

Gidan jaridar Triumph bai farfaɗo daga dogon sumansa ba sai da tsohon Gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya zama gwamna ne ya naɗa Kwamred Muhammed Garba, a matsayin Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa da Wasanni, sannan jaridar Triumph ta dawo ana buga ta duk mako saɓanin a baya kullu-yau-min.

A hankali Triumph ta ci gaba da bunƙasa, inda ta ke fitowa a ranakun Litinin, Talata, Laraba, Alhamis da Juma’a. A taƙaice ana cewa, Daily Triumph, duk da yake ranar Juma’a ta sha bamban da sauran ranakun, domin kuwa ranar Juma’a Albishir ta Hausar Boko take fitowa, sai Alfijir ita kuma da Hausar Ajami ake buga ta, wato baƙaƙen larabci ake buga ta da Hausa, wacce ita ce jarida irin ta kaɗai a duniya a irin tunani da basira na tsohaon Gwamna Kano Rimi (RH) ya samar.

Baya ga wannan, akwai Saturday Triumph, sai Sunday Triumph. Wato jaridu guda tara ke fitowa a duk mako a Gidan Sa’Adu Zungur, sunnan gidan da ake buga Triumph kenan a titin Katsina Road cikin ƙaramar Hukumar Fagge daf da tashar tsohuwar tashar Kuka a da ke birnin Kanon Dabon Nijeriya.

Wannan yawan jaridu a wannan gida ya sa jaridar Triumph ta zama ruwan jakara, wato idan mutum bai sha ba, an sha masa, domin kuwa kamar yadda aka faɗa a sama cewa, jami’a ce ta aikin jarida ga wanda ya san meye aikin jarida bisa la’akari da gogaggun ’yan jarida da Triumph ta fitar a Nijeriya, Afrika, da ma duniya bakiɗaya. Kaɗan daga cikinsu sun haɗa da Malam Garba Shehu, ma’aikaci ne kuma MD na Triumph ne tsohon kakakin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari; Kwamred Sani Zoro, tsohon shugaban ƙungiyar ’yan jarida na ƙasa (NUJ); Kwamred Muhammad Garba, tsohon NUJ na ƙasa kuma tsohon Shugaban ƙungiyar ’Yan Jarida ta Afrika ta Yamma (WAJA); Halilu Dantiye tsohon Shugaban ƙungiyar Editoci ta Nijeriya, da Mr Prince Ajayi, shugaban ƙungiyar NUJ na Kano na farko a tarihi. Akwai Mr Nda Isaiah, mahaifin Marigayi Sam Nda Isaiah, wanda ya kafa jaridar LEADERSHIP; akwai Malam Sule Yau Sule, tsohon kakakin Gwamna Malam Ibrahim Shekarau; akwai kuma fitattun ’yan jarida irinsu Malam Salisu Bichi, tsohon darakta a LEADERSHIP; Malam Kabiru Yusif, shugaban jaridar Daily Trust, Malam Abba Dabo, Marigayiya Bilkisu Yusif, Malam Adamu Aliyu Kiyawa, Malam Bash M. Bash, da irinsu Malam Aliyu Umar, mai aikin jarida da harshe uku idan ta kama; Larabci, Turanci da Hausa da Ajami yanzu haka. Akwai Malam Gali, editan Alfijir dake bayar da gudunmawa bayan ya yi ritaya.

Duk da wannan ƙoƙari na Triumph yanzu haka dai ba ta fitowa a takarda. A daidai wannan lokacin da gurguzun jaridun Kudu tsofaffi babu wacce ta koma ‘online’, kawai sai Triumph, duk da akwai masu cewa jaridun Kudu ne suka sa Arewa ta ɗauki mulki salim-alin ta ba wa Kudu a dawowar dimukraɗiyya da muke ciki a yau a 1999 zuwa yau 2026.

A yayin da wata majiya mai tushe ta tabbatar da cewa, jami’an hukumar gudanarwa sau uku suna zuwa kare kasafin kuɗinta duk shekara, amma babu ɗaya da aka aiwatar har yanzu tsawon shekara uku kenan a ƙarƙashin gwamnatin Abba Kabir Yusuf. Bayanai dai sun nuna cewa, kamfanin Triumph na fuskantar ƙarancin kayan aiki duk da irin tasiri da gudunmawar jaridar wajen ɗaga darajar mutanen Kano da ma Nijeriya bakiɗaya a fannin aikin jarida da ma sauran fannonin rayuwar al’umma bakiɗaya.

Wakilin Blueprint Manjaha ya nemi mai riƙon muƙamin Babban Daraktan na kamfanin jaridar, Malam Muhammad Hamisu Abdullahi, ta waya, inda ya tambaye shi a wane matsayi take a yanzu a hukumance, sai ya ce yanzu dai suna fitar da labarai kowacce rana a ‘online’, kuma Litinin da Juma’a su fito da labaran gabaɗaya na tsakanin waɗanan kwanakin, kuma sun rubuta wa gwamnati duk matsalolisu ta hannun Kwamishina Yaɗa Labarai, Kwamared Abdullahi Ibrahim Waiya kuma gwamnatin ta amince za ta aiwatar da duk wani abu da zai kawo wa Triumph cigaba. Haka sauran hukumomi masu ruwa da tsaki su ma sun tabbatar da kawo cigaban Triumph a Gidan Sa’adu Zungur In Zaka Faɗi Faɗi Gaskiya.

By ukarofi

Leave a Reply